Labarai

Yadda zaku Samu ‘Confirmation Message’ Daga NYIF

Kwanakin baya matasa sun cike “Nigeria Youth Investment Fund” ko “NYIF”, suka ce sun tura confirmation code zuwa email din mutane, amma hakika mutane da yawa basu ga sakon ba, ba’a tura musu ba, wanda ba’a tura masa ba, domin gyara wannan matsalar, sai ka shiga website din ? https://nyif.nmfb.com.ng/
Daga farko za ka ga Option guda uku.
1. Apply Now.
2. Loan Application.
3. Login.
Sai ka shiga ka danna wurin da aka rubuta “Login”, idan ya bude zaka ga ya kawo maka wurin da zaka saka Email dinka, ko BVN dinka, da kuma option na Password, toh kada ka shiga wannan wurin.
.
Kaje can kasa, zaka ga wasu kananan rubutu guda uku.
1. Forgot password.
2. Register.
3. Did not get verification Token.
Sai ka shiga wurin da aka rubuta “Did not get verification Token”.
Sai ka danna wurin, ka saka email dinka da kayi rijistan NYIF din dashi, sai ka danna submit, zasu ce maka successfully.
Sai ka jira na wasu awanni zasu tura maka da confirmation Link din bawai da kayi sau daya suke turawa ba koda sun tura maka da link bai zama dole yana da kyau ba kamar yadda kuke gani na tura musu sun turo min da comfiramtion link sau (16) amma har yanzu babu mai kyau.
Dole sai mutum yayi hakuri yai tayi har Allah ya bashi nasara.
Idan sun tura sai ka shiga email din ka danna, ka karashe har zuwa inda suke bukata.
Yi sharing don wanda suke jiran sakon Confirmation link subi wannan hanyoyin

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button