Kannywood

Rarara Yayiwa Tsofaffin Jaruman masana’antar Kannywood Goma Ta Arziki

Fitaccen mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara, ya yi wasu daga cikin tsofoffin masu sana’ar Finafinan Hausa kyautar naira dubu 50 ga kowane mutum daya.
A jiya Litinin Rarara ya zabi mutane 25, maza da mata wadanda suka dade a masana’anatar Kannywood, inda ya bada tallafin kudin na naira dubu 50 ta hannun makusantan shi, jarumi Tijjani Asase, da kuma Abubakar Bashir Mai Shadda, domin su damkawa tsofoffin jaruman.
Ga jerin sunayen jarumai maza da aka ba kudin.
1- Bashir Nayaya
2- Sani Idris (Moda)
3- Isah Bello Jaa
4- Sani Garba Sk
5- Baba Karami.
6- Hussaini Sule Koki
7- Baba Hasin.
8. Shehu Hassan Kano
9- Ashiru Nagoma
10- Baba Sogiji.
11- Abdu Kano (Karkuzu)
12- Umar Yahaya Malumfashi (Bankaura)
A Bangaren Mata kuma su je kamar haka:
13- Hajara Usman
14. Ladidi Fagge
15- Safiyya Kishiya
16- Asma’u Sani
17- Hadizan Saima
18- Mama Tambaya
18- Saima Muhammad
20- Ladidi Tubless
21- Fandi Borno
22- Baba Duduwa
23- Hajiya Sadiya
24- Lubabatu Madaki
25- Binta Ola Katsina
A cewar Rarara lokaci bayan lokaci, za a rika zakulo mabambantan mutane, wadanda ya kamata a tallafamawa a rika taimakon su.
Rarara dai ya yi kaurin suna wurin taimakon abokan aikin shi, inda lokaci bayan lokaci ya kan zabi wasu daga cikin abokan mu’amullar sa ya yi masu kyautar Motoci.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button