AddiniLabarai

Maganganu Shehu Dahiru Bauchi Sunyi Muni

Na saurari hiran da akayi da babban Malamin darika Shehu Dahiru Usman Bauchi akan ta’addancin masu garkuwa da mutane, daga cikin bayanan da yayi, yace ‘yan uwa fulani kashedinku da shiga kungiyar Izala kungiyar makiya Annabi (SAW)

Har yana ishara da cewa wai da ka shiga Izala yafi ka tsaya ka cigaba da ta’addancin ka, domin laifin kisan kai da kwace dukiyar mutane bata kai laifin kin Annabi ba, ‘yan izala ba Musulmi bane ku guje su.. inji Shehu Dahiru Bauchi

Ko a mafarki banyi tsammanin Shehu Dahiru zai fadi haka ba a wannan lokacin, me ya hada batun sharhinsa akan ta’addancin da kabilar fulani ke yi na garkuwa da mutane da Izala?

Ya sauka daga abinda ake masa tambaya a kai ya koma sukar izala, a Nigeria Manzon Allah (saw) bashi da masoya ‘yan a mutu masu kare masa martaba sama da ‘yan Izala, wallahi a kan soyayar Annabi da kare martabansa duk wani Musulmi a Nigeria sai dai ya biyo bayan ‘yan Izala

Wato na fahimci cewa akwai wasu miyagun mutane munafukai ‘yan kwangila da suke jikin Shehu Dahiru Bauchi, ana biyansu kudi suna hadashi hira da ‘yan jarida yana fadin abubuwa da ba su dace ba, tsufa ya hanashi gane cin amanarsa da ake, domin wannan cin amana ne

Ina ruwan kungiyar Izala da ta’addancin da wasu kabilar fulani ‘yan uwan Shehu Dahiru Bauchi ke yi?, muna ta kokari mu kare martaban kabilar fulani da ba su aikata laifi ba, shi kuma wannan yazo yana kokarin bata al’amura, ya kamata kafofin watsa labarai su takaita hira dashi akan mas’ala irin wannan

Haba Shehu akan Izala zaka huce haushinka bayan wasu gurbatattun kabilarka sun bata muku suna a idon duniya?

To Allah Ya sauwake!

Ga link nan domin kuyi Downloading

DOWNLOAD MP3
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button


WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?