AddiniLabarai

Kotu ta ƙi amince wa da buƙatar Malam Abduljabbar


Babbar kotun tarayya da ke Gyaɗi-gyaɗi a Kano bisa jagorancin mai shari’a Lewis Alagua ta ƙi amince wa da buƙatar lauyan Malam Abduljabbar Kabara.
Malam Kabara ya shigar da ƙara gaban kotun yana ƙalubalantar matakin sanya masa takunkumin hana wa’azi bisa zargin yana wuce gona da iri.
Yayin zaman kotun na yau Laraba mai shari’a Alagua ya ce, ba za a hana ƴan sanda da Gwamnatin aikinsu ba, saboda haka za a bar su su ɗauki mataki kan abin da suke ganin zai iya kawo barazana ga jama’a.


Kamar yadda Freedom radio kano na ruwaito. Wakilin mu na Kotu Bashir Muhammad Inuwa ya rawaito cewa, yanzu haka an ɗage sauraron shari’ar har zuwa ranar 18 ga watan Fabrairu da muke ciki, domin sauraron ɓangaren waɗanda ake ƙara.
Wanda ake ƙarar sun haɗa da Gwamnatin Kano da Babban Mai Shari’a na Kano da Kwamishinan ƴan sanda da hukumar tsaron farin kaya da jami’an Civil Defence.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button