Labarai

Yadda wani Malami ya Rika lalata da dalibar sa acikin Gidan sa tare bata Naira 500 har ya kai ga yi mata ciki a Jahar Katsina

A yau Majiyarmu ta samu wani labari mummuna daga shafin demokradiya sun wallafa wannan labari da malami ke amfani da dalibansa har da samun juna biyu.

Ga yadda sunka wallafa wannan labarin a shafinsu.

“Daga Wakilin mu na Jahar Katsina Usman Salisu Gurbin Mikiya

Wani Mataimakin Shugaban Makarantar Sakandare a cikin Karamar Hukumar Rimi ta jihar Katsina Ibrahim Tukur ya bayyana wa rundunar yan sandan jihar Katsina yadda ya rika lalata da wata dalibarsa, har ta kai ga ta haifar masa ‘Da Namiji.

Ibrahim wanda ya kasance Dan Asalin garin Kadandani ne, dake cikin Karamar Hukumar Rimi, yana koyarwa a Makarantar Sakandaren Al’umma ta Kadandani.

Ya kasance yana yiwa ‘Dalibar dabara Yar Shekaru 12, yana shigar da ita gidansa tare da yin lalata da ita har na tsawon watanni takwas.

A cewar Kakakin Rundunar Yan Sandan Jihar Katsina SP Gambo Isa, ya ce mahaifin ‘Dalibar da aka yi wa fyaden Ibrahim Sale shi ne ya kai korafin ga Rundunar Yan Sandan a Karamar Hukumar Rimi dake Katsina.

Tuni dai mataimakin shugaban makarantar ya amsa laifinsa, inda ya bayyana cewa ya yi lalata da yarinyar tsawon watanni takwas.

Kuma ya kasance Yana lalata da’ita a cikin gidansa da yake da mata uku a ciki, inda yake bata naira dari biyar , ko uku ko kuma naira dari biyu kacal.

Haka Zalika Rundunar ta gurfanar da wasu mutum hudu, da suka hada da Sa’idu Yahaya dake BCG Funtua, da kuma Lawal Sani dake Sokoto Rima Katsina, da Sani Kabir, dake Unguwar Makudawa a ciki garin Katsina dukkaninsu da irin wannan zargin na aikata laifin fyade ga kananan yara”.
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?