Labarai

Na karbi kudin fansa Milyan biyar 5m a hannun tsohon saurayina bayan nayi garkuwa dashi ~ Inji Budurwa Maryam

Rundunar ‘yan sanda a Kano a ranar Laraba ta gabatar da wasu mutane hudu da ake zargin masu satar mutane ne a cikinsu akwai wata budurwa’ yar shekara 23, Maryam Mohammed.

Ta furta cewa aikinta na farko a matsayin mai satar mutane ya fara ne da tsohon saurayinta wanda ya ki auren ta bayan sun yi shekaru suna soyayya

An kama Maryam Mohammed, wacce aka fi sani da Hajiya a makon jiya Talata tare da wasu mambobinta su uku a gidan Jaba, karamar hukumar Ungogo da ke jihar Kano ‘yayin tattaunawar neman kudin fansa da dangin daya daga cikin wadanda suka yi garkuwar da su.’

Ta ce kawunta, Hamza Dogo na ƙauyen Butsa, ƙaramar hukumar Gusau ta jihar Zamfara ne ya shigar da ita cikin wannan aika-aika bayan ta rabu da tsohon masoyin ta.

“Kawuna wanda ake kira da Hamza daga garin Butsa, karamar hukumar Gusau ta jihar Zamfara ne ya gabatar da ni cikin yin garkuwa da mutane kuma farkon wanda muka sace shi ne tsohon saurayina wanda ya ki ya aure ni duk da kokarin da na yi don ganin ya shawo kansa a tsawon shekarun da muka yi muna soyayya.

“Bayan ya jefar da ni, kawuna ya ce in kawo shi don mu rike shi har sai ya biya kudi kafin mu sake shi.

“Lokacin da muka sace shi, danginsa sun biya N5m don a kwato masa ‘yanci kuma daga cikin kudin an ba ni N800,000 wanda da shi na yi hayar wancan gidan da ke rukunin gidajen Jaba” Hajiya ta furta.

Kungiyar ‘yan ta’addan na daga cikin masu satar mutane da ke addabar garuruwan Zamfara da wasu sassan jihar Kano.

jaridar mikiya ta kara da cewa,Kakakin rundunar ‘yan sanda na Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa wanda ya gabatar da wadanda ake zargin ya ce binciken da’ yan sanda suka gudanar ya nuna cewa “an kashe mijin Maryam, mai suna Sani Ismail, na karamar hukumar Bidda da ke Jihar Neja,” wanda sanannen Mashahurin barawon Shanu ne, an kashe shi a Kauyen Butsa, karamar hukumar Gusau ta jihar Zamfara yayin da yake satar shanun barayin.

“Bayan rasuwar mijinta, dan uwanta, wani Hamza Dogo na kauyen Butsa, karamar hukumar Gusau ta jihar Zamfara, shi ma wani mashahurin mai satar mutane ya sake mata matsuguni zuwa Kano inda ta yi hayar gidaje a Unguwa Uku, Panshekara da Maidile Quarters.

”Daga baya ta koma gidan Jaba Quaters ta yi hayar wani gida a kan Naira Dubu Dari shida (N600,000.00), a kowace shekara, wanda ta mai da masu garkuwa da mutane aciki

“Sauran mambobin kungiyar sun hada da Sani Ibrahim da Shamsudeen Suleiman dukkansu na kauyen Butsa, karamar hukumar Gusau, jihar Zamfara da kuma Ishaq Khalil, wanda ake kira Baban Basma na Rijiyar Lemo Quaters, karamar hukumar Fagge ta jihar Kano.”
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?