Labarai

Masu Garkuwa Da Mutane Sama Da guda dubu 1 sun ajiye makamai Bayan Da Sheikh Ahmad Gumi Ya Ziyarce Su (Hotuna)

Babban Shehin Malamin Addinin Musulunci mazaunin Jihar Kaduna Sheikh Dr. Ahmad Mahmud Gumi, ya jagoranci wani zaman kawo daidaito a tsakanin Fulani don shawo kan sace-sacen mutane da Dabbobi a tsakanin Al’umma musamman su kan su Fulani.

A yayin ziyarar Sama da kwamandojin Daji (Shugabannin masu garkuwa da mutane) goma da tawagarsu sama da dubu 10000 suka yi alkawarin ajiye makamai, tare da fadan wadansu sharudda.

Hakan ya faru ne yau a Gundumar Kidandan, ciki karamar hukumar Giwa ta Jihar Kaduna.

Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewar Fulanin da masu garkuwa sun yi alkawarin Ajiye makamai, har ma sun bayyana wadanda suke basu makamai da kuma dalilan da suke yin wannan mummunan aiki.

Sheikh Gumi da tawagar sa sun yi alkawari zaa ginawa Fulanin Makaranta da Asibiti da kuma wajen neman Abinci.

Zaman kawo sasancin ya sami halartar Sheikh Ahmad Mahmud Gumi a matsayin Jagora da Kwamishinan Yan sandan Jihar Kaduna UM Muri da tawagarsa.

Har ila yau a tare da Malam akwai Shehunan Malamai ciki har da Sheikh Dr. Muhammad Sulaiman Adam da dai sauran su.

DIMOKURADIYYA
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?