Kannywood

Manyan jaruman Kannywood sun mayarwa Da Dr Bashir Aliyu Umar Martani

Mujallar Fim ta tuntuɓi manyan ‘yan fim da dama domin jin abin da za su ce kan wannan magana, amma da yawa sun noƙe a kan cewa ba su san hujjar da malamin ya dogara da ita ba.
Amma biyu daga cikin su sun yi magana, wato Alhaji Sani Mu’azu, wanda babban furodusa ne, jarumi, kuma tsohon shugaban ƙungiyar ƙwararru masu shirya finafinan Hausa (‘Motion Picture Practitioners Association of Nigeria’, MOPPAN).
Sani Mu’azu ya fara ne da yin tambaya, inda ya ce: “To wanda ya auri mace a fim fa?”
Ya ci gaba da cewa: “Ina ganin Malam ya yi tsauri a fahimtar harkar fim a nan. Mai yiwuwa saboda Hausawa kan kira aikin da sunan ‘wasan kwaikwayo’.
“Babu wasa a harkar fim. Sana’a ce wacce ba za ka yi fatawa a kan ta ba sai ka fahimce ta.
“Aure ibada ce bisa sunnah. Idan Malam zai alaƙanta abin da aka yi don faɗakarwa, to babu shakka wanda aka gani ya kashe mutum don faɗakarwa, shi ma Malam zai yanke masa hukuncin kisa.
“Ni ba malami ba ne, amma na san Allah SWT ya yi amfani da hankaka don ya yi dirama ta nuna wa ɗan’adam yadda zai binne ɗan’uwan sa.
“Allah SWT ya na amfani da niyyar mu ne a ko da yaushe. Don haka, Malam ya amince da niyyar mu ta faɗakarwa shi ma.
“Allah SWT ya yafe mana inda mu ke yin kurakurai, ya kuma ba mu ladar faɗakarwa inda ayyukan mu su ka wayar da kan mutane.”
Shi ma Hamisu Iyan-Tama da tambaya ya fara nasa tambihin, inda ya ce: “Idan har hakan ta tabbata gaskiya, to ina son Malam ya ba ni fatawa a kan idan kuma aka ɗaura aure, shi ma ya ɗauru?”
A wani saƙo da Iyan-Tama ya turo wa mujallar Fim, ya ci gaba da yi wa Sheikh Bashir tambayoyi kamar haka: “Idan mutum ya sha ruwa a matsayin giya (a fim) don nusarwa, shi ma giyar ya sha? Idan mutum ya rufe ƙofa da mace ya kashe fitala, shin zina ya yi turmi da taɓarya?
“Idan ɗan fim ya yi baccin wasa amma ba bacci ya yi da gaske ba, shi ma bacci ya yi? Idan ɗan fim ya fito a Kirista, ya na nufin ya zama Kirista kenan? Haka kuma idan Kirista ya fito a Musulmi, hakan na nufin ya musulunta kenan?”
Iyan-Tama, wanda furodusa ne, jarumi, kuma ɗan siyasa a Kano, ya ci gaba da ce wa shehin malamin: “Yanzu idan na fito a sheikh (a fim), ya na nufin ni na tabbata shehin malami? Idan na fito a shugaban ƙasa ko gwamna, hakan na nufin na tabbata ɗaya cikin biyun kenan?
“Idan na fito a matsayin Sheikh Dakta Bashir na Alfurƙan, hakan na nufin na zama shi kenan, da sauran misalai da dama?
“Kamar a fim ɗin ‘The Message’, Anthony Quinn ba Musulmi ba ne, amma ya fito a matsayin Sayyidina Hamza. Meye matsayin sa kenan?”
Iyan-Tama ya ce ya yi waɗannan tambayoyin ne domin ya na son ya ƙara ilmi don sanin yadda zai aiwatar da fim a nan gaba.
Wasu ‘yan fim kuma waɗanda wakilin mu ya kira a waya ba su ɗaga wayar ba.
Duk da haka, wasu ‘yan fim da su ka ce a sakaya sunan su sun ce ba su amince da wannan fatawar ta Sheikh Dakta Bashir ba.
Ba shakka, ‘yan fim na tsoron ja da malamin ne saboda batun ya shafi addini.
Majiyarmu Hausaloaded ta dauko wannan rubutu daga Fimmagazine.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button