AddiniFadakarwa

Hanyar Abincin Wani Malami zata kare Game Da Maganar Fulanin Daji Ya Fito Da Hassadarsa A Fili

Salisu hassan webmaster ne yayi wannan rubutu a shafinsa na sada zumunta wanda shine wanda ke kula da shafukan sada zumunta na sheikh Ahmad Gummi wanda wani babban malami yayi magana akan cewa abinda Sheikh Gummi Yayi baiyi komai ba.

Ga yadda ya wallafa rubutun nasa a shafin sada zumunta.

Jahili Murakkabi ke nan! Kace da Malamin da ya shiga daji karantar da Fulani da Gwamnan da ya ce su bar mishi kasarshi basu da banbanci. An ya malam be sha kwaya kuwa.

Muma bari mu sha tamu. Da malamin da ya ce kada a shiga daji a karantar da al’ummar fulani da shekau da yayi wa Dr. Ahmad Gumi barazanar kisa da cewa ya daina shiga daji duk daya suke.

Idan ba dan kwaya ba, yaushe mutane ana amfani da su (jahilan fulani) wurin yin ta’addanci, ana cutar dasu, ana talautasu, an samu wadansu bayin Allah sun dauki azamar wayar da kansu tare da gina musu Asibiti da Masallaci da makaranta amma kace wai wannan ta’addamci ne?

To idan ba a shiga daji an karantar da su ba, so kake a barsu a ciki har sai an gama hallaka su? Shin idan da ka dena shiga manyan motoci ana maka jiniya da fadanci ka shiga daji da tura mutane suna karantar da su da zasu yi wannan ta’addancin?

Da kake maganar kowace kabila tana da ‘yan ta’adda me yasa ba a kirasu ba? to me ya dame mu da ta’addancin wanda tun asalinsa dan ta’adda ne, mu abinda ya dame mu al’ummar Manzon Allah da aka sansu da girma da daraja da tsoron Allah da ilimi da kiwo da ake son su lalace itace ta dame mu kada ta lalace.

Kawai yanzu dai abinci ne zai kare a wurin mutanen da ake zuwa yi musu maula da sunan yin wa’azi ko yada da’awa, domin jama’a sun ce abinda ake yiwa ‘yan uwansu filani ya ishe su, kuma muna fatan abin ya tsaya

Ita fa hassada karshenta hauka ne, domin bata da magani sai Allah.

Allah Ya kare Sheikh Dr. Ahmad Gumi da sauran jama’ar da suke taya shi shiga daji da masu tallafa mishi a kowane irin gudunmuwa don ganin an wayar da kan Fulani.

Salisu Hassan Webmaster
08038892030
24/01/2021.”
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?