Labarai

Gwamnatin Jihar Rivers Ta Bayar da gudummuwar naira miliyan dari Biyar N500M Don Gyaran Kasuwar Jihar Sokoto Da Tallafawa Masu Gobara

A yau ne ranar labara 20/1/2021 Gwaman jahar rivers ya zo Sokoto domin jajantawa yan kasuwa jahar Sokoto da iftila’i gobara ya aftakawa a cikin babban birnin jahar Sakkwato waa babbar kasuwar Sokoto wanda shine Majiyarmu na samu labarin wannan kyauta daga makusancin gwamnan Aminu Waziri Sokoto akan lamuran yanar gizo ga abinda yake cewa

Maigirma Gwamnan jihar Rivers Nzenwo Nyesom Wike ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ziyarar ci babbar kasuwar Sokoto in da aka yi gobarar tare da Rakkiyar Maigirma Gwamnan jihar Sokoto Rt Hon Aminu Waziri Tambuwal CFR (Mutawallen Sokoto)

Gwamna Wike ya jajantawa wadanda abin ya shafa, inda ya bayyana duk abinda ya shafi jihar Sokoto to ya shafi jihar Rivers.

Tun farko Maigirma Gwamnan jihar Sokoto Rt Hon Aminu Waziri Tambuwal CFR (Mutawallen Sokoto) ya bayyanawa gwamna Wike adadin shagunonin da ke cikin wannan kasuwar da yadda abin ya faru.

Gwamna Tambuwal Amadadin al’ummar jihar sokoto ya godewa gwamna Wike akan wannan kokari da yayyi.

Muna fatar Allah SWT ya sakawa Maigirma Gwamna Tambuwal da mafificin Alkhairinsa, ya mayar da baki gida lafiya, su kuwa masu gobara Allah SWT ya mayar musu da mafificin Alkhairinsa don darajar Alkur’ani Maigirma

Bilya Yariman Barebarin Fcbk
Special Asst to Governor Tambuwal
Laraba 20th January, 2021″
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?