Addini

Dr Gumi: Wa’azi A Dokar Daji !!Dr Gumi, Shehu Buba Kun Cancanci Yabo (Hotuna)

Bayan takardar gaiyata da ziyarar da suka kawowa Dr Gumi wanda ya motsa himmarsa tare da gwada jarumtarsa da halin malinta na shiga daji don wa’azi da shiga tsakanin fulani yan tada kayar baya da Gwamnati, Hakan muke fatan ya zamo sanadin kawo karshen sace mutane da ilmantuwar fulanin !!
SHEHU BUBA UMAR (tsohon shugaban karamar hukumar Toro a jihar Bauchi) a matsayin barden boye a wannan tafiya ya cancanci yabo, wanda shine jagaban Dr kuma idonsa a wajensu!!
Kwamishinn yan sanda na jihar Kaduna yayi rawar gani don adadin fulani yan tada kayar bayan sun ninka jami’an da yaje da su kamar yadda yake a hoto amma ya saida ransa don Jama’a!!
Malamai masu wa’azi da Fulatanci Musamman daga yankin Karamar hukumar Toro da kuma cikin garin Jos da kewaye wadanda sune baraden yakin sojojin fadakarwa da Fulatanci sun cancanci yabo!!!
Allah ya sakawa kowa da alkairi ameen.
Wannan darasi ne ga hukumomi cewa Malamai nada babbar rawar da za su iya takawa wajen kawo warakar wassu cikin matsalolin kasarmu!! Dr Ibrahim disina ne ya wallafa wannan rubutu a shafin sa na Sada zumunta.
Sai kuma hukuma su cika alkawari!!

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button