Labarai

Da’awar zaman lafiya: Malaman Kirista na arewa sun jinjinawa Sheikh Gumi

– Malaman addinin Kirista a arewacin kasar sun jinjinawa Sheikh Ahmad Gumi kan da’awar zaman lafiya da yake yawon yi a dazukan Kaduna
– Gumi dai na bi mazaunin yan ta’adda yana wayar masu da kai a kan bukatar rungumar zaman lafiya a kokarinsa na kawo karshe kashe-kashe da fashi a Kudancin Kaduna
– Fasto Yohanna Baru ya ce yunkurin Gumi na yin da’awar zai taimaka sosai wajen daidaita matsalar tsaro a kasar
Kungiyar malaman Kirista na arewa sun yaba da kokarin da Sheikh Ahmad Gumi ke yi wajen samo mafita mai dorewa kan rashin tsaro a jihar Kaduna, jaridar Daily Trust ta ruwaito,wanda mu kuma Majiyarmu ta samu daga Legit.
Shugaban cocin Christ Evangelical and Life Intervention Ministry, Sabon Tasha, Kaduna, Fasto Yohanna Baru ya ce yunkurin Gumi na shiga dazukan Kudancin Kaduna don zantawa da makiyaya kan muhimmancin zaman lafiya da hadin kan kasar ya cancanci jinjina.
A cewarsa:
Allah ne kadai zai saka ma malamin Musuluncin a kan sadaukar da lokacinsa da yayi wajen ziyartan Fulani a jeji, sannan ya ja hankalinsu kan bukatar su karbi addinin Islama da ilimin zamani tare da kiwon dabbobi.
“Shi na daban ne kuma ya banbanta a tsakanin dukkan malamai da tsarinsa na kawo karshen kashe-kashe, fashin shanu, garkuwa da mutane, fashi da makami da sauransu.
“Don haka ya zama dole mun jinjina masa kan daukar wannan babban mataki da yayi wajen sasanci da ilimantar da matasan Fulani kan hatsarin da ke cikin ta’ammali da kwayoyi da aikata ta’addanci.”
Buru ya kara da cewa: “ba za a taba dauke kai ga muhimmancin zaman lafiya ba, saboda haka akwai bukatar su rungumi zaman lafiya, hadin kai da sasanci tare da gwamnati don magance masu matsalolinsu a kokarin kawo ci gaba a kasar.
Ya kuma yi kira ga malaman Musulunci da su yi koyi da kokarin Gumi sannan su samu lokaci don ziyartan Fulanin da ke zama a jeji don ilimantar da su da wayar masu da kai kan zaman lafiya.
Ya kuma yi kira ga kungiyar Jama’atu Nasril Islam da majalisar limamai da malamai a kasar da su hada hannu da Sheikh Gumi wajen tallata zaman lafiya ya mutanen da ke zama a jeji.
Hakazalika, Wani malamin Kirista, Reverend Paul Elisha Ham, ya roki masu hannu da shuni, shugabannin tsaro, kungiyoyi masu zaman kansu da su tallafa wa malamin Musuluncin wajen yada da’awar zaman lafiya a fadin jihohin arewa 19 da ke kasar.
Ya kuma bukaci gwamnatin jihar Kaduna da ta tallafa wa malamin da isasshen tsaro a duk lokacin da zai je jeji don yin da’awah.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button