Labarai

Babu Abinda Gwamnatin Buhari Tawa Yan Najeriya Inbanda Karya Da Yaudara ~ Farfesa Attahiru Jega

Tsohon shugaban hukumar zaben Najeriya Farfesa Attahiru Jega ya ce Gwamnatin Buhari ta watsa wa ‘yan kasar kasa a ido saboda gaza yin abin da aka zabe ta ta yi.
A wata tattauanwa da ya yi ta musamman da gidan jaridar Daily Trust, an tambayi Jega kan lamura daban-daban da suka hada da sake fasalin kasar, da kuma ra’ayinsa kan ta ina kuma ya kamata a fara.
An tambayi Jega ko maki nawa zai iya bai wa Shugaba Buhari kan rikon kamu ludayinsa.
Jega sai ya ce “Gwamnatin Buhari kwata-kwata ba ta yi abin kirki ba. Ya kamata ya yi abin da ya fi haka.
“Abin bai yi dadi ba, ya bai wa ‘yan Najeriya da yawa kunya. Amma har yanzu yana da lokacin gyara wasu abubuwan, amma idan zai iya kenan.
“Babu wani boye-boye, Gwamnatinsa ta ba da kunya. Mutane da dama sun yi ta yi masa fatan nasara amma yanzu suna nuna damuwa kan yadda kasar take tafiya,” in ji Jega.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button