Labarai

An ceto yara 18 da aka sata, amma har yanzu ba a neme su ba a Anambra (Hotuna)

Wadannan hotunan yara da ake gani ‘yan Gombe ne aka sace su, binciken ‘yan sanda ya nuna wata mata ce mai suna Hauwa Usman ‘yar asalin Gombe ta sace yaran ta kaisu jihar Anambra a ranar 20-10-2019 ta sayar wa inyamurai

Yanzu haka an samu yaran a inda aka sayar da su, suna hunnun ‘yan sanda a jihar Anambra, wasu iyayen yaran sun gane yaransu bayan da rundinar ‘yan sanda ta fitar da sanarwa, wasu yaran kuma har yanzu ba’a gano iyayensu ba

Ana kira ga jama’a da su taimaka waken yada wadannan hotuna ko Allah Zai sa a gano asalin iyayensu, ga nambar wayan kakakin ‘yan sanda na jihar Anambra CSP Haruna Muhammad 0813 591 4965 idan an kira za’a iya samunsa kowani lokaci

Idan da mutanen Arewa ne suka sace yaran inyamurai suna kawo su Arewa suna sayarwa da yanzu sun tashi hankalina kasa, ya kamata a dakatar da wannan cin amana da ake yiwa Arewa
Allah Ka isar mana.

Ga hotunan yara nan

 

 

 

 
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?