Wasanni

Mohamed Salah na shan suka daga wajan Musulmai bayan da yayi Murnar Kirsimeti

Tauraron dan kwallon kasar Egypt me bugawa kungiyar Liverpool wasa, Mohamed Salah ya taya Kiristoci Murnar ranar Kirsimeti.

Salah tare da iyalansa sun saka kayan bikin Kirsimeti inda ya saka a shafinsa na sada zumunta. Saidai wasu daga cikin Musulmai basu ji dadin hakan ba inda suka rika cewa bai kamata ba.

Hutudole sunyi kokarin fara tattara wannan bayyani a yayinda muma muka kara binciko wani ,Wani da ya bayyana ra’ayinsa akan hoton na Salah, ya saka Bidiyon wani mutum da yayi kokarin shiga wat kofa ta ki budewa, inda ya ce Salah ne yayin da yake kokarin shiga kofar Aljannah.

Wani kuwa me sunan Smiley ya bayyana cewa shiyasa yake son dan damben nan, Khabib Nurmagomedov a duk cikin shahararren mutane Musulmai, saboda ba zai taba yin wasa da addininsa ba dan farantawa wani, ya kara da cewa Musulmai basa bikin Kirsimeti.

Ya kara da cewa

Wanda yanzu haka idan kaje shafinsa zaka ga Musulmai na nuna alhinisu na nuna masa cewa wannan baida kyau
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button


WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?