Addini

Ku San Malamanku tare da Sheikh Abdulwahab Abdallah

Fitaccen malamin addinin musuluncin nan da ke birnin Kano a Najeriya Sheikh Abdulwahab Abdallah ya ce surorin da ya fi son karantawa a cikin AlƘur’ani su ne suratul iklas da ihsan da kuma sajadah saboda yadda suke burge shi.

Malamin ya bayyana hakan ne a hirarsa da BBC Hausa a shirinmu na musamman na Ku San Malamanku, inda ya ce hadisin da ya fi so shi ne wanda Manzon Allah ke cewa yana tare da mai sonsa ranar tashin alƙiyama.

“Wannan hadisin ko yaushe na wuce shi sai na gode wa Allah. Manzon Allah ba mu san shi ba amma a ranar tashin alƙiyama wanda yake son shi zai gan shi…wannan hadisin idan na karanta shi yana faranta min rai,” in ji Sheikh Abdulwahab.

Malamin ya ƙara da cewa ranar da ta fi sanya shi farin ciki a duniya ita ce lokacin da aka karɓe shi a Jami’atu Al-Islamiyya.

Sai dai malamin ya ce: “Amma babu abin da ke sanya ni baƙin ciki irin wanda ka amincewa ya je yana yi maka zangon-ƙasa.”

Malamin na addinin musulunci ya ce babu garin da yake so bayan Madina da Makkah kamar Kano.

“Ina son Kano saboda gari ne wanda za ka iya isar da saƙon da kake so na ilimi da addini, kana wanda ba ka da shi za a taimake ka,” in ji malamin.

Ya ƙara da cewa akwai malamai da ɗaliban ilimi waɗanda suka waye a Kano yadda ko da mutum ya yi kuskure za su fahimtar da shi cikin hikima.

Takaitaccen tarihinsa

An haife shi ranar 28 ga watan Agusta na shekarar 1953 a ƙasar Togo. Malamin, wanda ya ce shi Bawangare ne, ya tashi ne a hannun Limamin Waje da ke birnin Kano da ke arewacin Najeriya, Imam Umar.

“Wannan bawan Allah ko iyayena da suka haife shi ba su wahala da ni kamar shi ba,” in ji shi.

Ya soma karatu a wurin yayan mahaifinsa mai suna Imam Alhaji Yahya.

Daga bisani ya yi karatu a wurin babban malami marigayi Imam Ɗan’ammu da ke birnin Kano. Galibin karatun da ya yi a wurinsa sun shafi Riyadus-salihin da kuma Hadisai.

Kazalika ya ce ya yi karatu a wurin Sheikh Nasiru Kabara da Sheikh Shehu Maihula da Gida Shamsu inda akwai malamai irin su Malam Gali, da Malam Babba.

Malamin ya ce daga nan ne ya tafi Saudiyya tare da matarsa inda ya yi karatu a can. Ya ce ya yi karatu a wurin Sheikh Bn Bazz da Sheikh Uthaimin, waɗanda ya ce ya koyi halaye na gari da matuƙar tsoron Allah a wurinsu.
Dangantakarsa da marigayi Sheikh Ja’far Adam

Sheikh Abdulwahab ya ce shi da Sheikh Ja’far Mahmud Adam sun yi karatu tare inda suka mayar da hankali a kansa matuƙa.

“Ni da malam Ja’far mun yi alƙawari ba mu yarda mu shiga hukuma ba; da safe karatu, da yamma karatu. Abubuwan da suke hannunmu shi Malam Ja’afar (Allah Ya jiƙan shi) yana da abokanansa da ya ba su wani abu suna juya masa, ni kuma ina da almajirai na ba su wani abu don ina Saudiyya…ina sayar da mayafai, kafin in zo ina da kuɗi a hannuna sai na bayar ana juyawa,” a cewarsa.

Wanne abinci ya fi so?

Malamin ya ce tun da ya tashi babu abincin da yake so kamar tuwo yana mai cewa ba ya iya yin kwana biyu bai ci shi ba.

Tambayoyin da aka fi yi masa?

Shiekh Abdulwahab ya ce babu tambayoyin da aka fi yi masa kamar na “zamantakewar aure, duk bala’in a nan yake.”

A cewarsa: “Jiya jiyan nan ina zaune da hankalina mutum ya zo ina yi musu sulhu a gabana ya daki matarsa.”

Ya ce babu abin da ya fi sanya shi farin ciki kamar ya ga mutum ya Musulunta.

Ya ƙara da cewa babban abin da yake baƙanta masa rai shi ne idan “na ga ana fasadi.”

Shiekh Abdulwahab ya ce lokacin yana matashi ya yi wasa irin wanda matasa suke yi kuma ya saurari waƙoƙin turawa irin na James Brown da na ƙabilar Igbo da na larabawa “saboda waƙoƙi suna ɗaukar hankalin yaro.”

Sai dai ya yi gargaɗi da matasa da kada su bari waƙoƙi su janye musu hankali “domin suna maye gurbin karatu.”

Amma malamin ya ce ba ya sha’awar ƙwallon ƙafa.

Sheikh Abdulwahab yana da mata da ƴaƴa.

Babban burinsa

Da yake burin kowanne musulmi shi ne ya gama da duniya lafiya, shi ma Sheikh Abdulwahab ya ce babban burinsa shi ne “na cika da kalmar shahada.”
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?