Zamantakewar Aure

Da duminsa: Kotun daukaka kara ta jaddada hukuncin kisa a kan Maryam Sanda

Kotun daukaka kara da ke zama a Abuja ta tabbatar da hukuncin kisan da aka yanke wa Maryam Sanda a kan kisan mijinta Bilyaminu Mohammed Bello da ta yi.

Gwamnatin tarayya ta gurfanar da Sanda da wasu mutum uku a kan laifuka uku da suka hada da kisan kai.

Kamar yadda majiyarmu ta samu labarin cewa ,Alkali Yusuf Halliru ya yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya a ranar 27 ga watan Janairun 2020.

“Ta girbe abinda ta shuka, saboda an ce a kashe wanda ya kashe kuma duk wanda yayi kisa bai cancanci rayuwa ba,” Halilu yace.

“Wacce aka kama da laifin ta cancanci kisa, a don haka na yanke wa Maryam Sanda hukunci kisa ta hanyar rataya har sai ta mutu.”

Fusata da kuma rashin amincewa da Sanda tayi da wannan hukuncin ne yasa ta garzaya kotun daukaka kara domin bukatar sabon hukunci.

A bukatar da ta mika kotun daukaka karar ta hannun tawagar lauyoyinta, sun kwatanta hakan da tsabar rashin adalci.
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?