Labarai

Buhun shinkafa ya koma N19,000, masu boye kayan abinci sun shiga Uku

Masu tara kayan abinci suna boyewa domin sayar wa da tsada sun shiga uku domin kuwa kungiyar masu sarrafa shinkafa ta Nigeria, “Rice Processors Association of Nigeria”, RIPAN, ta ce amince ta karya farashin shinkafa zuwa Naira Dubu Goma Sha Tara, (50kg a N19,000)

Manuniya ta ruwaito sabon farashin zai fara aiki ne daga ranar 14 ga watan Disamba da muke ciki.

Babban jami’in RIPAN, Aminu Ahmed ya shaidawa jaridar Daily Nigerian cewa hakan na zuwa ne bayan ganawarsu da Babban Bankin Nigerian CBN, a wani mataki na rage radadin talauci da tsadar kayan abinci a Nigeria.

Manuniya ta ruwaito farashin buhun shinkafa a yanzu yana kaiwa daga N28,000, zuwa N35,000 ko ma fiye da haka.
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?