Addini

AUDIO : Taken Huduba: Mu Kiyaye Yada Fasadi A Bayan Kasa ~ Dr Bashir Aliyu Umar

HUDUBAR JUMA’A DAGA MASALLACIN ALFURQAN KANO 04/12/2020 – Dr. Bashir Aliyu Umar

Taken Huduba: Mu Kiyaye Yada Fasadi A Bayan Kasa

1. Masu kashe Musulmi da sunan Musulunci

2. Masu fashi da makami:

Allah ya siffantasu da cewa su masu yaki da Allah ne, masu yada fasadi. Allah yace ko a kore su, ko a kakkashe su, ko a tsire su.
Fashi da makami ya hada abubuwa 2, sata sannan da boye dukiya.

3. Taimakawa masu fashi da makami, hukuncin wanda ya taimaka musu tamkar shi ma ya yi fashi da makami ne, shi yasa Annabi ya hana sayar da makamai a lokacin fitina.

Wajibi ne wadanda suke taimakawa masu fashi da makami su nisantu, su daina, ko da matar aure ce ta ga mijinta yana irin wannan taimako to wajibi ne ta sanar da hukuma domin magance faruwar haka.

Dole ne mu taimaki junanmu, mu taimaki al’ummarmu wajen samun aminci a Kasarmu.

Manzon Allah SAW yace duk wanda aka kashe wajen tsare dukiya, wannan shahidi ne.
Duk wanda aka kashe wajrn tsare ransa, wannan shahidi nr.
Duk wanda aka kashe wajen kare iyalinsa wannan shahidi ne.

Babban tsarin da yafi komai shi mu tsare Allah da Manzonsa. Duk wanda ya tsare Allah to Allah zai tsare shi.

Wannan abubuwan suna da kyau mu kiyaye su:
1. Riko da Allah da Manzonsa.
2. Kiyaye sallar asuba a jam’i
3. Kiyaye mutuncin dan uwanka Musulmi.

Mu roki taimakon Allah domin abubuwan kasarmu suna ta tabarbarewa. Mu roki Allah da aminci da sunansa na aminci, kan Allah ya kawo mana aminci.

Mu dage da addu’a ga shugabanninmu wajen samar da aminci a Kasarmu. Allah madaukakin sarki zai tambaye su.

Allah ya ba mu albarkar wannan rana ta Juma’a, mu yawaita yin salati ga Annabinmu SAW.Allah ka amintar da mu. Amin

DOWNLOAD MP3
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?