Addini

Wasu Daga Cikin Littafan Da DR. Muh’d Sani Rijiyar Lemo Ya Rubuta Kafin Tafsir (Hotuna)

Daga Abdulrahman Muhammad Sharada
Allahu Akbar, hakika rayuwar Dr Muh’d Sani Umar Rijiyar Lemo a bar koyi ce, kuma Malam ya yi matukar bada gudummawa a fannin rayuwar Bahaushe. Musamman sboda irin jan aikin da ya yi na fassara alkur’ani da harshen Hausa wanda ba a taba samun irin sa ba a tarihi saboda yadda aikin ya gudana da kuma tsarin rubutun.
A cikin litaffan da Malam ya yi hakika wannan da aka gama a watan Disamba 2019 wato tafsir na Alkur’ani mai mujalladi shida, ya yi matukar daukar hankalina, ina matukar alfahari da kasancewa dalibinsa kuma mai halartar karatuttankasa.
Babu maganar akida ko bangaranci wannan aiki ya yi kyau kuma wallahi duk wanda ya yi wannan aiki ya cancanta a yabe shi saboda ya kara fito da martabar harshen Hausa.
GA WASU DAGA CIKIN LITTAFIN DA MALAM YA RUBUTA A RAYUWARSA
(1) Attamyìz (Tahqiqin Littafin Attalkhisul Habìr na Alhafiz Ibn Hajar,cikin Mujalladi Bakwai
(2) Dawãbid al-Jarhi watta’adíl.(Mujalladi biyu 2
(3) Almadrasatul Hadisiyya Fi Makkah Wal Madinah.(Mujalladi biyu 2 Manya-Manya).
(4) Bugyatul Mushtãq (Juz’i daya 1).
(5) Kitãbul Igrãb Na Al-imam Annasa’i (Tahqiqi) Juz’i daya.
(6) Nabiyyur-Rahma (Juz’i daya 1).
7) Attabsir Li Majalis Attafsir.
(8) Albinã’ul Ilmiy.
(9) Al-almãniyyah.
(10) Ithãf As-sãmi’i.
(11) Bugyatul Muhtãj.
(12) Alihtimãm Bissunnah.
(13) Tarihin Shaikh Usman Dan Fodiye.
14) Addìbãjah.
(15) Tamãm At-Taufiq (Tarihin Sayyiduna Abubakar R.A).
(16) Tarihin Rayuwar Malam (Hafizahullah) tare da Amininsa Shaikh Ja’afar (Rahimahulla)
Wadannan wasu daga cikin Littattafan da Dr Sani Umar Rijiyar Lemo (Hafizahullah) ya wallafa kenan, wadanda dukkan su an buga su, an fitar da su.
Akwai sauran Littafai da Malam ya ke rubutawa har yanzu, ba su kammalu ba, muna addu’a Allah ya karo mana irin Malam a wannan kasa ta mu da duniya baki daya.
Allah Ya karawa malam lafiya da nisan kwana,rayuwa tayi matukar albarka,Allah ya kare mana malam ya kiyayeshi a koda yaushe

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button