Kannywood

Rikici da Rarara kan matar aure: Abin da ya sa babu ruwa na – Afakallah

SHUGABAN Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Alhaji Isma’il Na’abba (Afakallah), ya bayyana abin da ya sa ba zai sa baki cikin batun zargin sa ake wa fitaccen mawaƙi Dauda Kahutu (Rarara) da saka wata matar aure cikin bidiyon waƙar sa mai taken ‘Jaha Ta Ce’.
Afakallah ya yi magana ne a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a ofishin sa a yau Juma’a.
Ita dai waƙar ta Rarara, an tsara ta ne don a nuna alhini kan tashin-tashinar rashin tsaro da ke garuwa a Jihar Katsina, kuma Ali Nuhu da Isa Alolo ne su ka bayar da umarni a wajen shirya bidiyon ta.
To sai dai a cikin wannan makon aka gano cewa ashe jarumar da Rarara ya saka a bidiyoin waƙar matar aure ce, kuma tuni mijin ta ya sha alwashin maka mawaƙin a kotu don a bi masa haƙƙin sa.
Mijin, mai suna Abdulƙadir Inuwa, ya shaida cewa auren su da Maryam dududu bai wuce watanni biyar ba, kuma ya sha alwashin maka Rarara a kotu domin ya saka matar sa a fim ba tare da izinin sa ba.
Tuni mijin jarumar ya garzaya Hukumar Hisbah ta Jihar Kano da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama don a bi masa haƙƙin sa.
Da ma dai tun tuni akwai ƙa’idoji da hukuma ta gindaya ga kowanne darakta game da matan da su ka cancanta a saka su cikin kowanne irin shiri don magance faruwar matsala irin wannan.
A hirar sa da ‘yan jarida a yau, Afakallah ya ce hukumar sa ba ta samu wani ƙorafi a kan batun na Rarara ba, kuma ba wani jami’i ko wata ƙungiya ko wani abu da aka kawo masu.
“Kamar yadda kowa ya gani a kafar sada zumunta, mu ma haka mu ka gani,” inji shi.
Ya ƙara da cewa, “Sannan abin da bai zo gaban ka ba kun ga ai ba za mu ce komai ba har sai mun ga abin da ya bijiro ko kuma aka zo da shi.”
A kan batun da wasu ke yi na cewa ko da an kai wa hukumar maganar gaban ta ba abin da zai faru saboda kusancin Rarara da Afakallah, sai shugaban ya yi dariya ya ce, “Ai kun san mutane kowa na da abin da ya ke cewa, ba kuma yadda za a yi ka hana mutum faɗar ra’ayin sa.
“Abin da babu shi ba a da tabbacin sa, sai idan har abin ya tabbata, don haka tun kafin a je ko’ina mutane sun ci Talata sun ci larabar abin, sun yi wa kan su hukunci. Don haka yanzu ba za mu ce a’a ko e ba a kan wannan zargi.
“Don haka sai abin da ya bijiro za mu tabbatar da yiwuwar sa ko rashin yiwuwar sa.”
Haka kuma a wani labarin, Afakallah ya bayyana cewa hukumar sa za ta fara saka ido a kan finafinai da waƙoƙin Hausa da ake ɗorawa a YouTube ne domin kiyaye yaɗa alfasha.
Ya kuma shaida cewa hukumar ba za ta naɗe hannu ta bari ana taka dokokin da su ka rataya a wuyan ta ba.
Shugaban ya yi wannan furucin ne yayin ganawar sa da ‘yan jarida a yau Juma’a bayan wani zama da su ka yi da masu ruwa da tsaki kan harkar ta YouTube da su ke a masana’antar Kannywood.
Afakallah ya ce mutane su na yi wa hukumar mummunar fahimta, sun manta cewa an kafa ta ne domin mutanen Jihar Kano.
Ya ce, “Ba wai mu na nufin mutanen da su ke Zamfara ko Abuja da sauran garuruwa da su ke harkar YouTube sai sun kawo an tace musu ba, a’a, da man Jihar Kano can ta fitar da tsari na Hukumar Tace Finafinai, shi ya sa mu ka tantance dukkanin wani mai ruwa da tsaki a Hukumar Tace Finafinai a 2019 wanda kuma wannan abin ya ba mu damar sanin ‘ya’yan mu.”
Ya ƙara da cewa, “Babu wani daga cikin ‘ya’yayen mu ko ma waye wanda zai saki wani abu a soshiyal midiya, ko ma ta wace kafa, face sai ya kawo abin sa mun tantance shi.
“Kuma abin nan da zai yi shi ne zai ba shi damar mu’amula da hukumar da kuma mu’amula da mutane domin kare addinin sa da al’adun su da kuma yanayin zamantakewar su.
“Kuma duk wanda ya halarci taron mun ba shi takarda ya rubuta mana adireshin sa na duk wata kafa da mutum ya ke amfani da shi, kama daga Instagram, YouTube, Twitter da sauran su.”
Idan masu karatu za su iya tunawa, kwanan nan mujallar Fim ta kawo labarin yadda Afakallah ya yi kira da kakkausar murya kan masu shirya finafinai masu dogon zango (series) waɗanda su ke ɗorawa a YouTube da su gaggauta zuwa su yi rajista da hukumar ga wanda ba su da ita.
Mujallar Fimmagazine ta kara da cwwa ,Shugaban ya ba wa masu sakin finafinan watanni uku don su gaggauta zuwa su yi rajista da hukumar.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button