Nafison In Rasa Rayuwata Da Baiwa Mutane Hakuri Martanin Bashir El Rufai ga masu sukar hotunansa da Nwakaego
Bashir El-Rufai ya ce masu sukarsa sakarkaru ne kuma ya gwammace a datse masa kai a maimakon ya nemi afuwar su
Bashir El-Rufai, ɗan gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya ce ‘ya gwammace a datse masa kai a maimakon ya nemi afuwa’ game da hotonsa da amaryarsa Halima Nwakaego Kazaure.
Tunda farko da an yi ta sukar Bashir saboda hotunansa da matar da zai aura da ya wallafa a Twitter.
A hoton na farko da ya wallafa a ranar Talata – an gano shi ya ɗora hannunsa a ƙugun Halima yayin da a hoton na biyu kuma suna rungume da juna yana sumbatar kumatunta.
Sai dai wannan hotunan bai yi wa wasu mutane daɗi ba musamman wasu musulmi da ke ganin abinda da ya aikata haramun ne.
Da ya ke martani game da caccakar da wasu ke masa a ranar Laraba, Bashir ya ce masu sukar su faɗa masa idan akwai wani abu da zai iya yi don ya ƙara musu haushi.
‘Idan hoto na da matata bai yi wa wasu dadi ba saboda shawararin da ban nema ba, ina son amfani da wannan damar in ce tabbas sakarkaru ne,’ kamar yadda ya rubuta.
‘Idan akwai wani hanya da zan iya ƙara ɓata musu rai, don Allah a sanar da ni. Wasu har yanzu ba su fahimci cewa ba kowa ne sukarsu ke tada wa hankali ba.’
Kamar yadda. Legit na ruwaito,bayan wannan wani mai amfani da Twitter ya masa tambaya ya ce, ‘Ina fatar ba za su saka neman afuwa ba don abinda ka faɗi.’
If my pictures with my wife does not sit well with some & due to the various unsolicited opinions, I’d just like to use this opportunity to say that they are very stupid & if there’s any other way these pictures can make them feel worse than they already do, please let me know.
— Bashir El-Rufai (@BashirElRufai) November 18, 2020
“Na gwammace a datse min kai a maimakon inyi hakan. Allah ya kyauta. Shashasha da ba za su iya fitowa su nuna kansu ba”, Bashir ya bada amsa cikin gaggawa.