Labarai

Muhimmancin saduwa Da Sanyin Safiya A lokacin Sanyi Ga Lafiya Da Walwalar Ma’aurata

Farfesa Musa Yakubu, na jami’ar Ilorin, a wata lakca da ya gabatar mai taken “Knocking Down the Barriers to Four O’Clock Activities” (Yaye Hijabin Da Ke Tsakaninka Da

Muhimman Al’amuran Karfe Hudu [na safiya]), ya bayyana jima’in sanyin safiya a matsayin wani makami mai linzami da zai iya tarwatsa rashin walwala, rashin jituwa, rashin fahimta da kuma uwa uba fatattakar matsalolin hawan jini da lalurori da suka shafi zuciya

Shehin malamin ya gabatar da kasidar ne a wajen taron gabatar da kasidun tabbatar da shehunnan malamai a matsayin farfesa mai cikakken iko karo na 163 na jami’ar ta Ilori da a turance a ke kira da “Professorial Inaugural Lecture”

Shehin Malami Musa Yakubu ya bayyana cewa, yin jima’i sau uku zuwa hudu a sati na taimakawa matuka wajen inganta rayuwar soyayyar ma’aurata, ya kuma kara danko da ingancin auren shi kansa
Farfesa ya ce ” Bincike ya nuna cewa jima’i na kara karfafa lafiyar garkuwar jiki ta hanyar samar da wani tsaro na musamman ga kwayoyin halitta hawa na farko da ke kare jiki daga kamuwa daga zazzabi da mashako (mura). Har-ila-yau, jima’i, na kara hauhawar kwayoyin halittar Immunoglobin A (IgA). Shi wannan Immunoglobin A na dauke da sindaran “Antibodies” da ke baiwa jiki wata kariya ta musamman daga kananun kwayoyin cututtuka dangin Bakteriya, da Bayros, da Tokzin (bacteria, viruses, toxins)”

Farfesa Yakubu ya ci gaba da cewa “Jima’i na taimakawa mace (matar aure) wajen daidaita lokacin al’adarta ya kasance babu tangarda tare da inganta samun lafiyayyen bacci”
Jima’i na sanya jikin dan adam ya saki wani sinadari mai suna Oxytocin da ke karawa mutum walwala da nishadi tare da inganta kusaci tsakanin ma’aurata biyu da kuma barinsu cikin farin ciki a duk lokacin da suka kammala jima’i”

Jima’i na tsawon minti 20 kacal na taimakawa jiki kona calories 150 (wani sinadari da ke samar da makamashin zafi ga jiki)
Farfesan na Biochemistry ya ci gaba da cewa “Jima’i shi ne mafi ingancin hanya da Ubangiji ya baiwa mutane don samar da nishadi, walwala da kuma karfafa dankon zumunci tsakanin ma’aurata”

Farfesa ya ce ” Duk auren da ma’auratan ba sa iya gamsar da junansu ta fuskar jima’i, aure ne da kai tsaye za ka iya kira da mataccen aure”
Rashin gamsar da abokin zaman aure, ko shakka babu ya yi sanadiyyar mutuwar aure babu iyaka a Nijeriya, a saboda haka Farfesa Musa Yakubu ya ja hankalin ma’aurata da su nemi hanyoyi sahihai na warware matsalolin jima’i a gidajensu.majiyarmu ta samu daga shafin abbanaseey

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button