Wasanni

Mohammed Salah Dan Wasan Liverpool Ya Kamu Da Cutar Corona

Ɗan wasan Liverpool Mohamed Salah gwaji ya tabbatar da yana ɗauke da cutar korona yayin da ya tafi bugawa ƙasarsa wasa

 

Hukumar ƙwallon Masar ce ta tabbatar a ranar Juma’a cewa Salah mai shekara 28, sakamakon gwajin korona da aka yi masa ya nuna yana ɗauke da cutar.

 

 

 

Hukumar ta ce sauran ƴan wasan gwaji ya nuna ba su ɗauke da korona.

Masar za ta karɓi bakuncin Togo a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin Afrika a ranar Asabar.

Yanzu Salah zai killace kansa kuma zai ƙauracewa buga wa Liverpool wasanni na tsawon mako biyu kamar yadda bbchausa na ruwaito.
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?