Labarai

Masar ta dakatar da wani farfesa daga aiki kan sukar Annabi Muhammad

An dakatar da wani Farfesan ilimin zamantakewa a Masar, bayan zargin da ake yi masa na yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW) yayin da yake gardama da ɗalibansa kan batun aure a Musulunci, da kuma bayyana ra’ayinsa a kafar sada zumunta kan zanen ɓatanci da Mujallar Charlie Hebdo ta yi ga Annabin.
Ɗaliban koyon ilimin zamantakewar sun bayyana ɓacin ransu kan irin kalaman da Farfesa Muhammad Mahdali ya yi yayin da yake bayyana ra’ayinsa.
Tun da farko dai, ɗaliban sun zargi farfesan da yin kalamai marasa daɗi kuma na cin mutuncin Musulunci yayin da yake koyarwa a aji.
A wani bidiyo da aka yaɗa a kafofin sada zumunta, an ga Farfesa Mahdaly na caccakar ayoyin Al-Ƙur’ani a yayin da yake wata tattaunawa kan batun aure da biyan sadaki da kuma saki a Musulunci.

biyan sadaki da kuma saki a Musulunci.

Kalli bidiyo a nan karin bayanai
Ci gaba da duba FacebookBBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba.

Karshen labarin da aka sa a Facebook, 1

BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba.
Karshen labarin da aka sa a Facebook, 1
An soma shari’ar mutanen da suka hari ofishin mujallar da ta yi ɓatanci ga Manzon Allah
Emmanuel Macron: Musulmi sun yi zanga-zangar kyamar Faransa bayan Sallar Juma’a
Ridda a Kano: An yanke wa mawaƙi hukuncin kisa bisa yin ɓatanci ga Annabi
Daga baya kuma sai ya yi sa-in-sa da ɗalibai a lokacin da yake koyar da su a ji a yayin da suka nemi su taka masa burki kan irin kalaman da yake yi, inda suka ja masa kunne kan cewa ya daina haɗa kalamansa da Al-Ƙur’ani.
A wani bidiyo na daban kuma, an ga farfesan na caccakar yanayin zamantakewar Musulmai inda ya ce abin da suke yi “ba shi da asali”. Har ma ya kawo misali da auren mata tara da Annabi Muhammad (SAW) ya yi kuma ya yi kakkausar suka ga Annabin kan hakan.
Wannan katoɓarar da farfesan ya yi kan batun caccakar ayoyin Al-Ƙur’ani da kuma nuna goyon baya ga kalaman Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya harzuƙa mutane da dama musamman a kafofin sada zumunta, inda suke ta caccakar farfesan.
Wasu daga cikin masu amfani da shafin Twitter sun alaƙanta farfesan da mutum mai laLurar “taɓin hankali”.
 


Wasu kuma na da ra’ayin cewa kwata-kwata ba SHi da addini, kuma bai yaRda da Allah ba.
Daga baya dai Farfesan ya bayar da haƙuri kan abin da ya yi kuma ya goge rubutun da ya yi.
Sai dai ministan ilimin gaba da sakandare a ƙasar ya bayar da umarnin dakatar da Mahdali kuma ya bayar da umarnin ƙaddamar da bincike a kansa.tattara bayyani bbchausa







Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button