Kannywood

Kurankus! Mawaki Rarara zai Gurfana a Kotu Akan Matar Aure Takarda Daga Kotu (Hoto)

Babbar Kotun shari’ar musulunci dake zamanta a ƙofar Kudu ƙarƙashin mai shari’a Ustaz Ibrahim Sarki Yola, ta tsayar da ranar 22 ga watan Disambar shekarar 2020 domin fara sauraron shari’ar da ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta shigar a kan mawaƙin siyasar nan Dauda Katuhu Rarara.
Ƙungiyar dai ta shigar da ƙarar ne a kan mawaƙi Rarara da tuhumar ɓoye wata matar aure mai suna Maryam Muhammad bayan da ya yi waƙa da ita a cikin bidiyon wata wakar sa da ya yi mai suna Jihata jihata ce, wanda a ka haura wata uku ba ganta ba.
Dimokuraɗiyya na wallafa,Kotun dai ta aike da sammaci ga mawaƙin domin ya gurfana a gaban kotun wadda za ta fara sauraron shari’a a waccen ranar da ta gayyace shi.
Kuma bayan fitowa daga kotun wadda ta zauna a ranar Juma’ar nan shugaban ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Global Cummunity for Humman Right Network, Ƙaribu Yahya Lawan Kabara, ya ce”Mun yi bakin ƙoƙarin mu wajen ganin mawaƙin ya zo wajen mu domin samun dai daito a tsakani, amma yaƙi zuwa, saboda haka mu ka shigar da ƙarar su a gaban Kotun, domin ta nemawa mijin matar haƙƙin sa”. Inji Ƙaribu Kabara.
Hakazalika shima mijin matar mai suna Abdulƙadir Inuwa ya roƙi kotun ta nema masa haƙƙin sa a kan waƙa da Rararan ya yi da matar sa cewa sam bai kyauta ba kuma ya ci mutumcin addini, inji shi.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button