Kannywood

Falalu Dorayi Yayi Jan Kunne Ga Masu Yada Labaran Karya

Babban daraktan masana’antar Kannywood falalu dorayi yayi jan kunne da jan hankali ga mutane masu yada labaran karya Da Jita jita a yau .
Wanda yayi a shafinsa na Instagram wanda daman jarumin ya sada da juma’a ga jawabin da ya wallafa.
L A B A R A N K A R Y A
Labaran karya da Jita-Jita Dabi’a ce da ta zamo ruwan dare cikin mutane, Lallai ne musulmi ya nisanci yada Jita-Jita da labaran karya, zancen da baka da tabbas ya faru amma ka bada labarinsa.
An bamu labarin DUJJALAWA
a karshen zamani, zasu dinga tsara Jita-Jita har sai wadansu mutane sun ringa daukar jita-jitarsu kamar fadar Alkur’ani.
Sharrin Jita-Jita da labaran karya suna haddasa fitina, gaba, kiyayya da rashin kwanciyar hankali tsakanin Al’umma. Sannan zata zamo TOZARTA ga wadanda suke yinta ranar ALKIYAMA.
UBANGIJI (SWT) Yace;
“Kuma kada ka bi abin da ba ka da ilimi game dashi. Lallai ne Ji da gani da zuciya, dukan wadancan(mutum) ya kasance daga gareshi wanda ake tambaya.”
Ga mai hankali sai ya kiyaye irin labaran da zai ringa dorarwa ga mutane, musamman a wannan lokacin da karyar tafi yawa a Labaran da muke karantawa.
Dukkan abin da bawa zai fadi ka tabbatar da sahihancin labari kafin ka yada shi a baki da baki Ko social media.
UBANGIJI (SWT) Yace;
“Ya ku wadanda suka yi Imani! Idan fasiki ya zo muku da wani babban labari, to, ku nemi bayani, domin kada ku cuci wadansu mutane a cikin jahilci, saboda haka ku wayi gari a kan abin da kuka aikata kuma masu nadama.”
Allah ka tsare mana harshenmu
Jum@tMbrk #sisters & #brothers”

 

View this post on Instagram

 

A post shared by F A L A L U A. D O R A Y I (@falalu_a_dorayi)Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button