Kannywood

Bidiyo : Matar Auren da ake Zargin Rarara ya sanya a wakarsa Tayi Magana

A makon da ya gabata ne, labarin wata mai suna Maryam Muhammad, ya karade kafafen sadarwa na zamani, inda aka rika zargin fitaccen Mawakin Siyasa Dauda Kahutu Rarara da sanya Matar Aure a cikin bidiyon wakar sa mai taken Jihata Jihata ce, ba tare da sanin mijinta ba. Haka zalika a an bayyana cewa shi mijin nata, ya sha alwashin maka Rarara a Kotu domin a bi masa hakkinsa na amfani da matarsa ta aure da aka yi .
 
 
Abdulkadir Inuwa shi ne mijin Maryam Muhammad, a wata hira da ya yi a shirin `Inda Ranka` na gidan rediyon Freedom Kano, ya bayyana cewa a yanzu haka ya kai koken sa a Hukumar Hisbah ta jihar Kano da kungiyoyin kare hakkin bil’adama don a bi masa hakkinsa.
 
 
Sai dai a wani dan karamin bidiyo da a Kannywood Exclusive ta samu a shafin Maryam Aliyu ‘Yar Fim, mun ci karo da bayanan wadda ake zargin Matar Aure ce, ta fito ta karyata lamarin, inda ta ce sharri ne kawai ake son yi wa Rarara, ta kuma kara da cewa a yanzu haka ba ta da aure, shi mijin nata da ya fito yana wannan maganganu yana so ne ta koma gidan shi saboda sakin wulakanci da ya yi mata.
Ga bidiyon nan kasa ku kalla.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button