Kannywood

Batun Gina Masallacin Hadiza Gabon Ran Jaruman Kannywood Ya Ɓace

A yau dai ne anka samu labari harda bidiyo na nuna wani masallaci da hadiza aliyu gabon tayi wanda anka wallafa a shafukan sada zumunta.

Ashe duk da nuna hakan yasa jarumi kuma babban daraktan shirya fina finai Abdulmuminu tantiri yayi dogon rubutu a yayinda shima jarumi ali nuhu yayi copy ya sanya a shafinsa duk a Instagram wanda ya nuna cewa duk ra’ayin su daya.

 

Ga rubutun da jarumin ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Duk da cewa musulunci yayi hani da yada alfasha,Ina ganin inda alummar mu suka fi karkata kenan,daga masu posting zuwa masu comment a kafafen yada labarai na social media,Burinsu ace Dan film ko yar film sunyi laifi su yada a duniya da tsinuwa da la’anta,.Abin mamaki Wannan baiwar Allah Hadiza Gabon tayi abun alkhairi kamar yanda kuke gani na duba kafafen da sukayi suna wajen batanci da son yada laifin yan film banga sunyi wannan posting ba,inda akayi posting dinma idan ka duba comment session zakaga mutane kalilan ne,Hakan yasa na tambayi wasu masu posting laifin yan film cewa ‘yaya naga bakuyi posting wannan abun alkhairi ba?Sai sukace mun wai ai tsakaninta da Allah ne,To shi laifin idan yan film sunyi Ubanku suka yiwa?Naga dai gara ka yada alkhairi da ka yada sharri,domin shi mai yada laifi cikin alumma yafi mai laifin kasanta.Annabi S.A.W yace ku fadi alkhairi ko kuyi tsitt,Allah ya saka da alkhairi malama Hadiza.”

 

 

View this post on Instagram

 

A post shared by ALl NUHU (@realalinuhu)
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?