Kannywood

Batanci Ga Annabi : Yadda Sufeto Janar ya umarci kwamishina ya kama Rahama Sadau

SUFETO-JANAR na ‘Yansandan Nijeriya, Alhaji Mohammed Adamu, ya ba Kwamishinan ‘Yansanda na Jihar Kaduna umarnin ya binciki Rahama Sadau kan iƙirarin da aka yi cewa ta aikata saɓo a kan Manzon Allah (SAW).
Sakamakon wannan umarnin, kwamishinan, Alhaji Umar Muri, ya gayyaci fitacciyar jarumar ta Kannywood da Nollywood da ta gabatar da kan ta a ofishin sa a yau.
Wata ƙwaƙƙwarar majiya da ke kusa da binciken da ‘yansanda ke yi kan wannan magana ta faɗa wa mujallar Fim ɗazu ɗazun nan cewa yanzu haka Rahama ta na kan hanyar ta ta zuwa ofishin kwamishinan daga Abuja.
Majiyar ta ce a da, jarumar ta na kan hanyar ta ne ta zuwa ƙasar Dubai ita da mahaifiyar ta da ƙannen ta uku – Fatima, Aisha da Zainab.
Idan kun tuna, a safiyar yau jaridar Muryar ‘Yanci ta buga labarin cewa ‘yansanda sun kama Rahama a Abuja a lokacin da ta ke ƙoƙarin tserewa daga Nijeriya. To amma majiyar mujallar Fim ta ce duk da yake ‘yansanda sun nemi su kama jarumar a Abuja, ba a yi hakan ba saboda wani babban hafsan ‘yansanda mai muƙamin kwamishina ya sa baki a cikin maganar, inda ya buƙaci a dai bari ta kai kan ta ofishin kwamishina da kan ta, “ba tare da an tozarta ta ba.”
Hakan ne ya sa jarumar tare da mahaifiyar ta da dangin ta su ka bar Abuja ɗazu, su ka kama hanyar komawa gida Kaduna inda Rahama za ta je ta ga kwamishina.
Majiyar mujallar Fim ta ce: “Nan da ƙarfe uku mu ke sa ran Rahama za ta iso hedikwatar ‘yansanda a Kaduna.”
Ita dai Rahama, Sufeto-Janar ya sa a bincike ta ne saboda wata takardar koke da wani mutum mazaunin Abuja mai rajin kare haƙƙin ɗan’adam ya rubuta masa a kan cewa wai jarumar ta aikata saɓo a kan Annabi Muhammadu (SAW).
A takardar koken da mutumin mai suna Alhaji Lawal Mohammed Gusau ya rubuta, wadda mujallar Fim ta samu kwafe, an buƙaci Sufeto-Janar da ya sa ya a kama Rahama saboda wasu hotuna da ta tura a soshiyal midiya sun haifar da aikata saɓo da wani mutum ya yi a kan Manzon Allah.
A takardar, mai ɗauke da kwanan wata 3 ga Nuwamba, 2020, Alhaji Lawal ya faɗa wa Sufeto-Janar cewa lokacin da hotunan da Rahama ta tura su ka haifar da ka-ce-na-ce, jarumar ba ta gaggauta cire su daga shafukan ta ba, maimakon haka sai ma ta nuna cewa ta ji daɗin muhawarar da hakan ta haifar.
Ya ce: “Ran ka ya daɗe, wannan ya haifar da tashin hankali kuma zai iya jawo tarzoma domin kuwa matasa da wasu malaman addinin Musulunci sun fara barazanar cewa su fa za su ɗauki mataki a kan ta.
“Ran ka ya daɗe, idan aka yi la’akari da abin da ya faru kwanan nan a Kano da kuma kwana kwanan nan a Faransa, yanzu an riga an kai al’ummar Musulmi maƙura.
“Za ka amince da ni, ran ka ya daɗe, kan cewa Nijeriya ba za ta iya jure wani sabon rikicin addini ba a daidai lokacin da ba ta gama murmurewa daga rikicin zanga-zangar SARS ba.
“Saboda haka, ina kira a gare ka da ka sa a kama wadda ake zargin sannan a yi cikakken bincike a kan lamarin. An ce gyara kayan ka ba zai zama sauke mu raba ba.”
Wata majiya ta shaida wa mujallar Fim cewa Lawal Gusau ya aike da kwafen wannan takarda tasa ga fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi a Sokoto da kuma wasu manyan mutanen Nijeriya.
Sakamakon wannan koke da Lawal ya yi, shi kuma Sufeto-Janar ya rubuta wa Kwamishinan ‘Yansanda na Jihar Kaduna umarni inda ya haɗa da takardar koken, kuma ya umarce shi da ya gaggauta yin bincike a kai.
Takardar umarnin da Sufeto-Janar ya ba kwamishina
A takardar umarnin mai lamba 7000/IGP.SEC/ABJ/VOL.508/313 da kuma kwanan wata 3 ga Nuwamba, wadda Babban Jami’in Ofishin Sufeto-Janar  mai suna DCP Idowu Owohunwa ya rattaba wa hannu, an faɗa wa kwamishinan cewa: “Ina sanar da kai umarnin da Sufeto-Janar na ‘Yansanda ya bayar cewa ka gaggauta ɗaukar mataki don tabbatar da cewa wannan lamari bai haifar da wani abu na rashin tsaro da tada hankalin jama’a ba.
“Haka kuma Sufeto-Janar na ‘Yansanda ya bada umarnin cewa ka riƙa sanar da shi duk wani abu da ya biyo baya kan wannan al’amari.”
Yanzu dai ba a sani ba ko ‘yansanda za su riƙe Rahama ne da sunan za su yi bincike ko kuma za su ɗauki jawabin ta ne su sake ta. Sannan ba a sani ba ko za su maka ta a kotu ne.
Amma wani na hannun daman ta ya faɗa wa mujallar Fim cewa jarumar ta tuntuɓi lauyan ta wanda zai take mata sawu zuwa hedikwatar ‘yansandan.
Shi dai Alhaji Lawal Mohammed Gusau sananne ne wajen shiga al’amuran da su ka shafi harkar finafinan Hausa. Idan an tuna, al’amari na baya-bayan nan da ya shiga ciki shi ne da ya kai ƙara a kan bidiyon tsiraici na Maryam Booth wanda aka yaɗa a soshiyal midiya a ‘yan watannin baya.
Daga :Fimmagazine







Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button