Labarai

Batanci Ga Annabi (Saw) ! wata Kotu A Kano Ta Fara sauraren Daukaka Karar Aminu Sheriff

Wata babbar kotun jihar Kano ta fara sauraren daukaka karan da Zindiki Aminu Sheriff ya daukaka bayan ya samu taimakon lauya daga kungiyoyin yahudawa akan kalama batanci da yayi wa Annabi Muhammad (SAW) wanda wata kotun Musulunci ta zartar masa da hukuncin kisa

Kotu ta fara sauraran karan ne cikin yanayi na tsatsauran tsaro a yau Alhamis 26-11-2020 karkashin jagoranci alkalai guda biyu, babban alkalin Kano mai shari’a Nura Sagir Umar da kuma mai shari’a Nasiru Saminu

Lauyan Zindiki Aminu Shariff Barista Kola Alapinne ya kalubalanci hukuncin kisan da kotun shari’ar Musulunci ta yanke wa Aminu Sheriff, yana mai cewa hakan ya saba wa kundin tsarin mulkin Nigeria, inji tsinannen Lauyan

Lauyan ya nemi kotu da ta yi watsi da hukuncin kotun shari’ar Musuluncin sannan ta saki Aminu Sheriff yaci gaba da rayuwarsa

Sai dai lauyar da ke wakiltar gwamnatin Kano, Barista Aisha Mahmoud (‘Yar Aljannah Insha Allah) tayi kira ga kotun da ta tabbatar da hukuncin da kotun Musulunci ta yanke a kan zindiki Aminu Sheriff

A nasu bangaren, alkalan kotun sunce nan gaba za’a kira lauyoyin bangarorin biyu a sanar da su ranar da za’a yanke hukunci

Ya Allah Ka tsine ma wannan lauya albarka da wadanda suka dauki nauyinsa
Allah Ka dusashe tasirinsu
Allah Ka tarwatsa al’amarinsu
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?