Kannywood

AN YANKA TA TASHI: Matar Aure Dauda Kahutu Rarara Ya Saka A Matsayin Jarumar Wakar Jahata Ce

Daga Indabawa Aliyu Imam
An gano cewa jarumar da shahararren mawaki Dauda Kahutu Rarara ya yi amfani da ita a shirin wakarsa mai taken ‘JAHATA CE’ Matar aure ce, kuma sunanta Maryam Muhammad kuma tuni mijinta ya sha alwashin maka mawaki Rarara a kulliya manta sabo domin a bi masa hakkinsa na amfani da matarsa ta aure da aka yi kamar yadda ya bayyana min.
Wakar jahata ce an tsara ta ne bisa nuna alhini na tashin-tashinar rashin tsaro da jahar Katsina ke fama da shi tunda jimawa, wanda jarumi Ali Nuhu da Isa Alolo suka bayar da umarnin shirya ta, akwai fitattun ‘yan wasa irin su Baballe Hayatu da suka fito a cikinta.
Abdulkadir Inuwa shi ne mijin jaruma Maryam Muhammad ya shaida mana cewa aurensu da Maryam dududu bai wuce watanni biyar ba, kuma ya sha alwashin maka mawaki Rarara a gaban kotu don amfani da aka yi da matarsa ba tare da izininsa ba, wanda yanzu haka tuni mijin Jarumar ya fara garzayawa hukumar Hisbah ta jahar Kano da kungiyoyin kare hakkin bil’adama don a bi masa hakkinsa.
Dama dai tuntuni akwai ka’idoji da sharadai da aka ce Hukuma ta gindaya ga kowanne darakta game da matan da suka cancanta a yi amfani da su wajen daukar kowanne irin shiri don magance faruwar matsala irin wannan.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button