Labarai

An kaddamar da mota mai amfani da batiri mai caji ta farko a Najeriya a garin Lagos (Hotuna)

Daga Sani Twoeffect Yawuri

Ita dai wannan motar kamfanin Stallion Motors ne ya hada ta anan gida Najeriya

Asalin motar Yar kamfanin Hyundai Kona ce kuma tana dauke da lamuni wato warranty na akalla shekara biyar (5)

Idan akayi cajinta kuma zata iya yin awanni goma (10) tana aiki kafin a sake yin cajin batirin ta

Idan zakayi tafiya da ita na awanni kamar bakwai (7), misali daga Lagos kaje Benin, har zuwa Asaba a Jahar Delta kudin cajin batirin ta naira dari uku da goma sha shida (N316) ne kacal.

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya jagora ci bikin ƙaddamar da motar da ke amfani lantarki irinta ta farko ta Najeriya.

A wannan Juma’ar ce gwaman ya ƙaddamar da motar mai suna Hyundai Kona a yankin nan na Ojo da ke jihar Legas, inda aka ƙerata.

Motar dai za ta riƙa amfani ne da chajin da za a riƙa mata a matsayin makamashi maimakon man fetur da motoci suke amfani da shi a ƙasar.

Ya kuke kallon wannan cigaban da aka samu?

Ga hotunan nan kasa ku kalla.
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button


WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?