Kannywood

A Ina Hadiza Gabon Ta Samu Kudin Gina Masallaci?

A Yau ne shahararren marubucin nan Datti Assalafy yayi wannan rubutu akai wanda jiya ya nuna irin yadda jaruma hadiza Gabon yayi abun alkhairi ne sai mutane suke tambaya da mamaki shin kowa yasa irin yadda al’amarin su yake ba hanya ce mai kyau ba shine dalilin shin wannan rubutun nasa.

“Tun bayan tabbacin labarin da muka samu cewa Hadiza Gabon ta gina Masallaci muka yada saboda kasancewa abin alheri ne, sai mutane suke ta tambaya cewa a ina ta samu kudin gina Masallaci?

Wasu suna cewa kudin da ta gina Masallacin ba na halal bane, wato ana munana mata zaton cewa ta samu kudin ne ta hanyar banza kamar yadda ake ganin haka yana faruwa a gurin matan da suke wasan kwaikwayo, don haka kudin najasa ne, akwai hadisin da yace Allah mai tsarki ne baya karba sai abu mai tsarki

Don Allah ‘yan uwa masu sukar Hadiza Gabon don ta gina Masallaci shin akwai wanda yake da tabbacin ta samo kudin ne ta hanyar karuwanci kamar yadda kuke munana mata zato?

Ina ganin bai kamata a damu da batun ta ina ta samo kudin ba, wannan ya rage tsakaninta da Allah, don haka muyi mata adalci akan abinda muka gani tayi na zahiri wato gina Masallaci sai muyi mata fatan alheri

Bayan haka akwai wani Malami da yayi jawabi akan Masallacin da Hadiza Gabon ta gina, ya kawo fatawowin Malamai guda biyu, Malami na farko yake ganin bai halatta a gina Masallaci da kudin haram ba, dayan Malamin kuma yana ganin halaccin haka, har ma yace mafi rinjayen Malamai sun tafi akan halascin hakan

Wannan babban kalubale ne ga matan da suke wasan kwaikwayo, hakika ba sana’ace mai kyau ba musamman ga mace, abin tsoro ne ace kina yin sana’ar da ba ta dace ba, wanda duk abinda kikayi na alheri sai aga ai kin samo kudin ne ta hanyar banza

Yaa Allah Ka shiryar da su Hadiza Gabon Ka basu ikon yin aure, Ka tsare al’ummah daga sharrin masu sana’ar wasan kwaikwayo Amin.”
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

7 Comments

  1. Allay ya saka mata da mafificin Alkhaeri ya bata ikon dorewa akan abubuwan Alkhaeri shine fatana ga dukkan Musulmin duniya baki 1

  2. Lallai Kam tayi abun ayaba mata,yadda ta samo kudi wannan hukuncine tsakaninta da Allah, Allah ya Saka mata da alkhairinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?