Labarai

Zanga-zangar SARS: Bidiyo Mafusata sun afkawa Fadar sarkin Legas, sun kori jami’an tsaro tare da dauke sandar sarautar sarkin

Rahotanni daga birnin legas sun bayyana cewa mafusatan matasa sun afkawa fadar sarki Legas dake Iga Idugaran a Legas Island.
 
An ga matasan na lalata motoci da dama inda kuma suka kwashi kayayyaki suka tsere dasu.

Wani shaida ya gayawa Punch cewa matasan sun fara kaiwa gidan mahaifan gwamnan jihar harine inda ‘yansanda suka kashe wasu daga cikinsu amma sai suka sha karfin ‘yansandan suka tilasta musu guduwa, bayan sun kona gidan mahaifan Gwamnan sai kuma suka zarce zuwa Fadar sarkin legas din inda suka afka mata.
 
Ga bidiyon nan kasa.







Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button