Labarai

Yadda saurayina ya rabu da ni saboda ni mata-maza ce

Shin yaya za ku ji a matsayinku na mahaifa idan aka wayi gari kun haifi mata-maza? Watakila amsar ta kasance ‘Allah ma ya kiyaye’.
A wasu kasashe musamman wadanda suka ci gaba, hakan ba abin boyewa ba ne ballantana har a yi gori, watakila saboda bambancin al’ada da fahimta da kuma ci gaban fasahar zamani a likitance.
 
kamar yadda bbchausa na ruwaita,Sai dai a arewacin Najeriya, mata-maza da mahaifansu kan kasance cikin yanayin tsangwama da gori.
Abokin aikinmu, Khalifa Shehu Dokaji ya tattauna da mai halittar mata-maza da ke son komawa cikakkiyar mace, wadda muka yi wa lakabi da Tarasulu.
 
“An haife ni da al’aurar namiji da mace duk da cewa a lokacin bangaren mace ya rinjayi na mazan. A lokacin mahaifina ya kai ni asibiti amma saboda rashin wadata sai aka bar ni ba tare da an yi min aiki ba,” a cewarta.
Ta kara da cewa bayan da ta girma sai al’aurar maza take kara girma a jikinta.
A cewarta: “Yanzu shekarata 25 da haihuwa amma ba ni da mama sannan al’aurar maza ce ke kara girma. Amma da al’aurar mata nake yin fitsari. Kuma ba na yin jinin al’ada sannan ba ni da mama kamar mata.”
Tsangwama
Matashiyar mai shekara 25 ta ce irin tsangwamar da take fuskanta a tsakanin kawaye da sa’anni ce ta sa ta hakura da shiga cikin mutane sannan ta daina zuwa makaranta.
 
 
Ta ce: “Akwai wani saurayi da na taba yi wanda har an fara maganar aure amma da aka sanar da shi cewa ni mata-maza ce sai ya gudu. Yanzu dai ina da samari har guda uku amma ba su san ina da halittar mata-maza ba. Amma zan sanar da su kafin a maimata abin da aka yi a baya. Sannan yanzu ni na daina zuwa makaranta ma saboda tsangwama da zolaya.”
Babban burin Tarusulu shi ne ta zama cikakkiyar mace domin samun damar yin aure kamar kowacce mace.
“Burina na koma mace ta yadda ni ma zan yi aure kamar kawayena. To amma kasancewar mahaifana ba su da karfi nake rokon al’umma da su taimaka min,” in ji ta.
Labarin Tarasulu dai daya daga cikin irin kangin rayuwar da masu halittar mata-maza suke ciki a arewacin Najeriya.
Bayanai na nuna cewa a yanzu haka dai da dama masu halittar mata-maza suna barin karatu a jihar Kano saboda irin tsangwamar da suke fuskanta.
Arewacin Najeriya ne dai koma baya ta fuskar ilmin zamani a Najeriya, kuma da alama tsangwamar da masu halittar mata-maza ke fuskanta a tsakanin ‘yan uwansu dalibai ka iya zama silar ta’azzarar al’amarin a yankin. Yadda tattaunawa bbchausa da tarasulu ta kasance kenan.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button