Labarai

Yadda Aka Yi Wa Sabon Sarkin Zazzau Mubayi’a Bayan Yi Masa Nadi

Yadda Aka Yi Wa Sabon Sarkin Zazzau Mubayi’a Bayan Yi Masa Nadi
Daga Muhammad Sadis, Zaria
Bayan sanar da sabon Sarkin Zazzau a jiya Laraba da aka yi da nada shi wanda sakataren gwamnatin jihar Kaduna ya jagoranta a fadar Masarautar Zazzau, yau alhamis 8/10/2020 , sabon Sarkin ya karbi mubaya’a daga hakimai da sauran gungun jama’a na masarautan Zazzau.
Bayan zaman Sarkin a majlisa da misalin 11:00 na safe, babban Limamin Zazzau ya gabatar da addu’a, sai aka fara kiran sunaye don yin mubaya’a.
Iyalan marigayi Sarkin Zazzau Shehu Idris ne suka fara karkashin babban su wato Turakin Zazzau, inda kusan dukkan ‘ya’yan marigayin sun yi mubaya’a ga sabon Sarkin.
Gidan Barebari (Kaura) su ma sun yi mubaya’a, Walin Zazzau ne ya jagoranta, Sarkin Malamai, Durimi, Karfen Dawaki, Katukan Zazzau duk suna cikin wadanda suka yi mubaya’a daga gidan Barebari.
Gidan Katsinawa karkashin Wamban Zazzau, Alhaji Abdul Karimu Aminu, Sarkin Daji da sauran Hakiman gidan Katsinawa duk sun yi mubaya’a.
Gidan Mallawa dangin sabon Sarkin duk sun mika wuya karkashin Wambai.
Unguwanni da manyan gidaje da daidaikun malamai duk sun isa fadar Zazzau din don nuna goyan baya.
Tsohon gwamnan Kaduna, Dallatun Zazzau da jami”an tsaro suna cikin wadanda suka yi mubaya’a.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button