Labarai

Wakilan Yarbawa Sunci Amanar Shugaba Buhari A Zanga-zangar #Endsars – Datti Assalafy

Wakilan Yarbawa Sunci Amanar Shugaba Buhari A Zanga-zangar #Endsars – Datti Assalafy

Hakika su Bola Ahmad Tinubu, Gwamnan jihar Lagos da sauran shugabannin yarbawa wadanda suke ci a gwamnatin nan sunci amanar shugaba Buhari

Ina ganin alamar sun hango 2023 cewa yarbawa ba su da takaran shugaban kasa shiyasa zasu yiwa shugaba Muhammadu Buhari butulci tun daga yanzu

Na rantse da Allah yadda na san yarbawa da dabi’ar girmama shugabannin su inda ace zasu fito su tsawatarwa su Sowore masu kitsa wannan zanga-zangar to da sun dena, amma sunyi shiru, asalima cikin wadanda suka fara zanga-zangar ENDSARS har da gwamnan jihar Lagos

Gwamnatin nan kamar ta yarbawa ce, a zahiri shugaba Buhari ya fifita yarbawa sama da kowace kabila a Kasar nan, duk wani aikin alheri daga yankin yarbawa yake farawa, amma yau gashi nan suna saka masa da butulci

Shugaba Buhari ka farga, wakilai da mukarraban shugaba Buhari ku farga, ku hada kai ku samar da mafita, imba haka ba mulkin ku yana rawa, komai zai iya faruwa

Allah Ya sauwake
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?