Labarai

Tashin Hankali ! Zanga-zanga A Birnin Maiduguri (Hotuna)

 
Yanzu haka dubbanin mutane a birnin Maiduguri na jihar Borno sun fito zanga-zangar lumana don nuna fushinsu akan rushe rundinar SARS da gwamnatin Buhari tayi, suna kira da a dawo da SARS a jihar Borno.

Daga jiya zuwa yau an rufe manyan hanyoyi na jihar Borno da ake zuwa wasu garuruwa saboda yanayi na tsaro sakamakon rushe rundinar SARS da akayi, saboda yawancin direbobi basa bin hanya idan basu ga dakarun SARS suna patrol ba.
 

Matakin rushe SARS ya tayar da hankalin Gwamna Zulum, saboda ya yadda da SARS sosai, duk inda zai je a gururuwan jihar Borno su ke bashi kariya, idan an yi masa harin kwanton bauna su ke sakashi a cikin motarsu na sulke, to yanzu an rushe su
Da alamar gwamna Zulum zai gana da shugaba Buhari akan matakin rushe SARS saboda amfanin da suke yi a jihar Borno
Allah Ka kawo mana mafita na alheri AminMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button