Addini

Sheikh Bala Lau yayi kira ga masu ce-ce kuce akan Gayyatar Sheikh Jingir zuwa Hadejia, da su daina

 
Director na kasa a gefen shafukan sada zumunta na jibwis   Ibrahim Baba Suleiman ne ya bayyana hakan a shafinsu na jibwis
Shugaban JIBWIS Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau,yayi kira ga marubuta musamman na dandalin ‘FACEBOOK’ dake tafka muhawara akan gayyatar da aka aikewa Sheikh Jingir zuwa wajen aza tubalin gina jami’ar AS’SALAM’ Mallakar kungiyar IZALA. Sheikh Bala Lau yace babu dalili da za’a yi hakan a musulunci, laifi ne babba a dinga cin mutuncin juna.
 
 
Shugaban ya kara da cewa, Nasara muke nema a wajen Allah, kuma mun samu, to me zai sa ka biyewa wani wanda bai fahimci hakan ba, inaga yakamata mu maida hankali akan abun da ya shafe mu, maimakon nemawa kawuna zunubi.
 
”Daga yanzu Ina umurtan wadanda ke rubutu da sunan masu kare mu cewa, kada kowa ya sake irin wannan rubutu ga kowaye, ku mutunta kowane Malami. Idan wani ya fadi sharri akan mu, to ku, ku fadi alheri akansu,. mu ci gaba da neman yardan Allah. Mungode.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button