Labarai

Mun ɗaura ɗamarar yaƙi da aƙidun addinin Islama – Faransa

 
Ministan cikin gida na Faransa Gerald Darmanin ya ce Faransa na yaki da akidun Islama, bayan kashe wasu mutane uku a wata coci da ke kudancin birnin Nice.
Ya yi gargadin kara samun irin wadannan hare-hare, sai dai ya jaddada cewa Faransa ba ta yaki da wani addini.
Bbchausa na ruwaito cewa jagoran ‘yan adawar kasar Marine Le Pen ta yi kira ga gwamnati ta bijiro da dokokin gaggawa don tasa keyar masu kaifin kishin Islama zuwa kasashensu na ainihi.
Shugaba Emmanuel Macron zai sake gudanar da wani taro na majalisar tsaro don tattaunawa game da harin Nice da kullen korona, wanda ya fara aiki da tsakar dare.
Wanda ake zargi da kisan na birnin Nice na cikin mawuyacin hali a asibiti bayan ‘yan sanda sun harbe shi.
 

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button