Labarai

Masu zanga zangar #Endsars Sunki Amincewa Da Sabuwar RundunarSWAT

 

Sakataren zanga-zangar ENDSARS Olufemi Sunday yace:
Hakika shugaba Buhari ya raina hankalin mu da matsayin mu na ilimi, rushe SARS muke so yi gaba daya, rainin wayo ne a canja musu suna a dawo dasu cikin awanni 24…

 

“…sabbin jami’an tsaron SWAT da yace ya kawo SARS ne kawai ba kowa ba, ta yaya za’a rushe jami’an tsaro a ‘kasa da awanni 48 kuma ace har an kawo sabuwar hukuma, ba za mu daina zanga zangar ba…” ~inji Sakataren ENDSARS Olufemi Sunday.

 
Datti Assalafy ya kara da cewa ,wato asali wadannan mutane ba manufarsu zanga-zangar rushe SARS bane, fakewa sukayi da SARS, amma juyin juya hali suka fara RevolutionaryNow da niyyar kifar da gwamnatin Buhari, don haka sai gwamnati ta rufe ido ta dauki mataki, imba haka ba za’a ga abu marar kyau
Allah Ya sauwake

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button