Labarai

Kayi Amfani Da Fasahar ICT waje Yakar Ta’addancin Kasar nan- Tambuwal Ga Buhari

A satin da ya gabata ne tawagar gwamna a jahar Bauchi ne yayi wannan furuci inda Majiyarmu na samu daga jaridar Legit hausa, ga bayyanin nan.
Ya yi wannan furucin ne yayin hirar da ya yi da ‘yan jarida lokacin da shugaban PDP na kasa, Uche Secondus ya jagoranci wata tawaga zuwa jihar Bauchi don kaiwa gwamnan ziyara a ranar Juma’a.
Tambuwal ya bayyana damuwarsa kan rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma inda ya ce akwai karancin ‘yan sanda ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya ta dauki matasan da suka cancanta aiki a hukumomin tsaro.
Ya ce, “Ina kira ga shugaban kasa ya duba yiwuwar daukan matasa da suka cancanta aiki. Muna da matasa da dama masu kishin kasa marasa aikin yi da za su iya shiga aiki irin na ‘yan sanda, Soji, DSS da sauran hukumomi.
 
“Ina kira ga Shugaban kasa ya duba yiwuwar daukan wadannan matasan da suka cancanta domin mun san akwai karancin jami’an tsaro a Najeriya, akwai bukatar kari. Na san muna kokari kan batun ‘yan sandan unguwa amma hakan ba zai wadatar ba.
Kazalika, muna kira ga Shugaban kasa ya samar da fasahar sadarwar zamani wato ICT ga dakarun mu da ke yaki da ta’addanci, ‘yan bindiga, masu garkuwa da sauran laifuka.”
Sauran wadanda ke tawagar sun hada da Secondus, mataimakin shugaban PDP na kasa shiyyar Arewa, Nazif Gamawa, tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark da tsohon gwamnan Gombe, Ibrahim Dankwambo.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button