Labarai

Kayan Agajin Da Aka Gani A Sito A Legas Ba Namu Ba Ne ~  Sadiya Farouk

 
Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya ta bayyana cewa kayan agajin zaman annobar korona da aka gani a wani babban sito a Legas ba nata ba ne.
Minista Sadiya Umar Farouq ce ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da ta bayar a ranar Alhamis.
An riƙa yaɗa maganganu a soshiyal midiya cewar waɗannan kayan agaji mallakar ma’aikatar ne, wai Hajiya Sadiyar ce ta kimshe su ta ƙi a rabawa ga mabuƙata.
Amma a martanin da ta yi kan wannan ji-ta-ji-tar, ministar ta ce, “Wannan ba wani abu ba ne illa zuƙi ta malle.
“Hotuna da bidiyoyin da aka ɗauka daga babban wurin aje kayan sun nuna cewa buhunan shinkafa da sauran an rubuta ƙarara a jikin su cewa ‘Lagos State Government and Ca-Covid’.
“To, ‘Ca-Covid’ a taƙaice na nufin ‘Coalition Against Covid-19’, wanda wata ƙungiya ce mai zaman kan ta da ta yi haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayya, Cibiyar Yaƙi da Cututtuka ta Nijeriya, da Cibiyar Lafiya ta Duniya (WHO) da nufin yaƙi da annobar korona a Nijeriya.”
Ministar ta jaddada cewa ba ma’aikatar ta ba ce ta samo kayan agajin ƙungiyar ‘Ca-Covid’ tare da rarraba su ko ta taimaka wajen raba su kan wannan tsarin.
Ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da irin wannan labarin, kuma ta ce babu ruwan ma’aikatar da kayan agajin da aka gani a wannan babban sito ɗin na Legas. Rariya ta wallafa hakaMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button