Labarai

Kalli Hotunan Yanda Rana 3 ta fito a kasar China a Yau

Wani gari a Kasar China a safiyar, Alhamis ya ga abin mamaki inda Rana ta rabe zuwa gida 3 kuma a Lokaci guda.
 
Ranar ta tsaya a haka har tsawon awanni akalla 3. Abin ya farune a wani gari me suna Mohe dake kusa da iyakar kasar da Rasha.
Shafin Hutudole na ruwaito,lamarin ya farune daga Allah, amma dai su masana sun saka masa sunan Sun Dogs wanda ba kasafai ya cika faruwa ba a kasar.
Abin ya faru daga karfe 6:30am zuwa 9:30 na safiyar yau. Ma’aikatar kula da yanayi ta kasar ta saka hotunan a shafinta inda aka ga haske guda 2 a sama.
 
Ga hotunan nan kasa.
     Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button