Labarai
Gwamnatin Da suka shude na sanya Nigeria halin da Take ciki Ina kokarin fitar Da ita ne ~ Buhari
Gwamnatin Obasanjo, Yar’Adua Da Jonathan Ne Suka Sanya Nijeriya Cikin Halin Da Take Ciki, Wanda Nake Ta Kokarin Fitar Da Ita Daga Ciki, ~ Buhari
A yau ne ranar Alhamis 1st ga watan October 2020 ake murna shekara 60 da samun incin kai.
Wanda yayi jawabi karfe 7 na safe wanda yayi wannan bayyani kamar yadda Majiyarmu ta samu daga shafin Rariya.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zargi gwamnatocin baya tun daga 1999-2015 cewa sune suka saka Nijeriya cikin halin kakanikayi da ya sa har yanzu ana fafutikar yadda za a fiddo ta ne daga wadannan matsaloli ne wanda gwamnatin sa ke yi ba dare ba rana, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Wadanda suka shugabanci Najeriya daga 1999-2015, suka gurgugunta ne wai yanzu ke da bakin cewa bamu yin wani abin a zo a gani ba a mulkinmu.