Labarai

An Fara Kaurace Wa Kayayyakin Faransa Kan Batanci Ga Addinin Musulunci

Daga Comr Abba Sani Pantami

Faransa ta janye jakandanta daga kasar Turkiyya, yayin da shugaba Recep Tayyip Erdogan ya zafafa caccakar takwaransa Emmanuel Macrona gameda kalamansa a kan Musulunci, inda yake cewa ya je a duba lafiyar kwakwlwarsa.

Faransa da Turkiyya dai sun shiga yi wa juna kallon hadari kaji ne a game da batutuwa da suka hada da rikicin gabashin tekun Mediterranean, Libya da Syria, da kuma kan yakin da ake gwabzawa tsakanin Armenia da Azerbaijan.

Amma abin da ya fi harzuka Turkiyya shine kudirin Macron na kare manufofin Faransa a matsayin wacce babu ruwanta da harkokin addini daga ayyukan masu tsatsaurar ra’ayin Islama, lamarin da ya sa Erdogan ya bukace shi da ya je a duba lafiyar kwakwalwarsa, yana mai karawa da cewa ba ya tsammanin zai kai gaci a zaben Faransa mai zuwa.

Wadannan kalaman na Erdogan suka sa Faransa, a wani mataki na bas a bam bam ta yi wa jakadanta a Turkiya kiranye, don ya gana da Macron.

Wani jami’in fadar gwamnatin Faransa na Elysee wanda baya so a bayyana sunansa ya ce, kasar ta lura da rashin samun sakon jaje kan fille kan wani malamin tarihi, Samuel Paty daga shugaba Erdogan.

A cikin wannan watan ne Macron ya bayyana cewa addinin Musulunci na cikin rikici a fadin duniya, inda yake cewa gwamnatinsa za ta gabatar da wani kudiri da zai karfafa dokar nan ta 1905 da ta rabe tsakanin majami’a da harkokin kasar a hukumance.

Tuni wasu kasashen musulmi suka fara janye kayayyakin Faransa daga shagunansu, bayan kiran da Turkiya da wasu kasashen larabawa sukayi na a kaurace musu.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?