Labarai

Ministan Sheikh Pantami Ya Wakilci Buhari A Wajan Kaddamar Da Tubalin Gina Jami’ar AS-Salam Global University A Garin Hadejia

 
Majiyarmu ta samu daga shafin rariya inda daya daga cikin editan dinsu ya wallafa da nuna hoyunan halarcin ministan sadarwa da tattalin arzikin nigeria dakta Isah ali ya wakilci Shugaban kasa Buhari ga jawabin da ya wallafa.

Ministan Sadarwa da tattalin Arzikin Nijeriya Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami, ya wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari, a wajan bikin aza harsashin gina jami’ar AS-Salam Global University a garin Hadejia dake jihar Jigawa.

Mai girma, Shugaba Buhari ya kasance shine bako na musamman a wurin taron, yayin da Sarkin Musulmi, Mai Martaba Muhammad Sa’ad Abubakar, ke matsayin shugaban taron.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Mai masaukin baki Gwamnan jihar Alhaji Muhammad Badaru, da Gwamnonin jihohin Sokoto, Kebbi, Katsina da Kano da wasu tsoffin gwamnonin jihar Zamfara.

Membobin majalisar dokoki, sarakunan gargajiya, shugabannin addinai da manyan jami’an gwamnati, da dai sauransu, sun samu halartar taron.

Dakta Pantami, babban masani a fannin kimiyar fasahar sadarwar zamani tare da gogewa a fannin sanin tattalin arzki na fasahar sadarwa da ƙwarewa, wajan ci gaban abubuwan cikin gida kuma gwarzo, ana sa ran zai kawo gogewarsa da hangen nesan sa wajen tabbatar da Jami’ar ta samu cigaba na zamani daidai da karni na 21.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button