Labarai

Rarara Ne Ya Dace Ya Taimaka Mana Ba Mu, Mu Taimake Shi Ba ~ Indabawa Aliyu Imam

Ban hana kowa ya turawa Rarara kud’i domin buga wa’ka ba, domin kowa akwai irin tunani da hangen da Allah ya bashi a karan kansa, shi dai Rarara ba talaka ba ne, tuni ya riga ya fi karfin abinda zai kai bakinsa, za ku shaida hakan yadda yake ta rabon motoci da babura, kai talaka da ke fama da abinci kai ne abin tausayi, amma ba ka taimaki kanka, ‘yan uwanka ko sauran jama’a ba, sai ka turawa wani mawaki naira dubu daya don ya buga wa’ka.

Da yawan masu tura wannan kud’i da za ka titsiye su ba za su iya kawo maka wata shaida ba wacce za ta nuna sun ta’ba taimakon wani mabu’kaci ko majinyaci da ya nemi taimako daga garesu da naira dubun da suke turawa  don ayi wa’ka ba.

Ko kun san naira dubun da ake rainawa kudi ce wacce da ita za’a iya ceto rayukan mutane da dama?  Musamman idan aka duba masu fama da matsananciyar rashin lafiya da wadanda za’a musu aiki amma Allah bai hore musu ba,  irinsu suna nan da yawa suna fama da rad’adi da zugin ciwo, ‘Kungiyoyi da gidauniyoyi nawa ka sani wadanda ke nemawa irin wad’annan bayin Allah taimako? Shin me zai sa ba za ka tura musu ta ka gudummar ba domin fitar da wadannan bayin Allah daga mummunan yanayi da suke ciki sai ka turawa wanda bai cancanci a turawa ba? Shin amfanin me wa’kar za ta muku duniya da lahirarku?

Mutane nawa ka sani ke cikin mawuyacin hali suke bukatar taimako koda na d’ari biyar ne? Akwai magidanta da marayu da ke tsananin bukata wanda za ku faranta musu zuciya idan kuka basu wannan naira dubun amma ba ku yi haka ba sai kuka turawa wanda bai cancanta da ita ba.

Mutane nawa ruwan sama ya lalata musu gidaje da mahallai suka koma yawon gararamba suke bukatar gyara muhallansu basu sami iko ba? Me zai hana ba za ku tara musu wannan kudi don su sami ingantacciyar rayuwa kamar yadda ku ke yi ba?

Ina Zawarawa da marayun Katsina, Zamfara, Sokoko da Borno wadanda ‘yan ta’adda suka kashe musu mazaje da iyaye su ke cikin mummunan yanayi na rashin gata da bukatar taimako? Ina ‘yan gudun hijira? Ashe ba su ne su ka fi cancanta a taimaka musu ba? Me ya sa ba za’a yi gangamin taimakawa wadannan bayin Allah da dubu dubu don a sama musu ingantacciyar rayuwa ba?

Kai magidanci a karan kanka idan har ba za ka taimaki mabu’kata da wannan dubu dayar ba, zai fi kyau kayi amfani da ita wajen kyautatawa iyalinka ta hanyar siyo musu wani abun dad’i ko kayan marmari, idan ka yi haka har a wajen Allah ka na da lada.

Duk wanda ya tura wannan dubu daya ya sani bashi da ladan sisin kwabo, ya salwantar da kud’insa a iska, ya dace yayi istigfari, masu almubazzaranci ba wasu bane face ‘yan uwan shaidanu, kuma yadda ka salwantar da dukiyarka ma abun tambaya ne ranar gobe kiyama.

Muna kira ga ‘kungiyoyi da sauran masu fad’a aji, da su yi amfani da irin wannan dama wajen nemawa mabu’kata da majinyata mafita, idan har mutane irinsu Rarara ba su ji kunyar fitowa su nemi a tura musu dubu dubu ba, ku da kuke taimako bai kamata ku ji kunyar jama’a su tura dubu dubu ba.

Allah ya ganar da mu.

Indabawa Aliyu Imam

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button