Labarai

LABARI MAI DADI: Farashin Kayan Abinci Ya Soma Ruftowa Kasa Warwas A Wasu Sassan Nijeriya

ALHAMDULILLAH

Rahotanni daga wasu kasuwannin kananan hukumomi a jihar Taraba sun tabbatar da faduwar farashin kayan abinci.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar farashin kayan abincin ya fara faduwa a garuruwa kamar haka, Mutum Biyu, Garba-Chede, Maihula, Dakka, Garbabi, Tella Monkin da Jatau.

KASUWAR MAI HULA: Masara sabuwar girbi a kan farashin N8000.

KASUWAR DAKKA: Masara sabuwar girbi  N7000.

KASUWAR MUTUM BIYU: Sabuwar Masara 12,000

KASUWAR GARBA CHEDE: Sabuwar Masara 11,000

Farashin sabuwar shinkafa ‘yar gida ya sauko daga N17,000 inda a yanzu ake sayar da duk buhu guda a kan N12,000.

Karyewar farashin kayan hatsin na zuwa ne a yayin da manoma a fadin jihar ke ci gaba da girbi bayan samun yabanyar amfanin gona.

A yanzu dai ana sayar da duk kwano daya na shinkafa ‘yar gida a kan N900 sabanin yadda aka rika cinikayyarsa a kan N1,200 a makon da ya shude, cewar Daily Trust

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button